logo

HAUSA

Dandalin APEC ya mayar da hankali kan tattalin arzikin yanar gizo don bunkasa ci gaba bayan annobar COVID-19

2020-11-20 11:18:24 CRI

Jami’ai, da shugabannin masana’antu da masana, sun bayyana cewa, tattalin arzikin yanar gizo ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ci gaba, yayin da ake fama da annobar COVID-19, baya ga yadda tsarin zai kara samar da damammaki ga ci gaban yankin Asiya da Fasifik da zai kunshi kowa da kowa a nan gaba.

Masana da jami’an sun bayyana haka ne, a jawaban da suka gabatar jiya Alhamis, yayin bude taron dandalin shugabannin kungiyar APEC na wannan shekara.

Dandalin APEC ya mayar da hankali kan tattalin arzikin yanar gizo don bunkasa ci gaba bayan annobar COVID-19

A jawanbinsa na bude taron dandalin, shugaban hukumar bunkasa harkokin kasuwancin kasa da kasa ta kasar Sin, (CCPIT) Gao Yan, ya bayyana cewa, tattalin arzikin yanar gizo, da masana’antu na zamani gami da hidimomi ta yanar gizo duk sun taka gagarumar rawa, a yakin da kasar Sin ta yi da annobar COVID-19, gami da tsarin samar da kayayyaki mai dorewa. Yana mai ba da misali da rawar da bangaren ba da hidima na fasahar sadarwa ta zamani na kasar Sin ya taka a cikin watanni 9 na farkon shekarar 2020, yana mai cewa, tasirin tattalin arzikin yanar gizo na karuwa a kowace rana.

Alkaluman da ma’aikatar kula da masana’antu, da fasahar sadarwa ta fitar ya nuna cewa, sashen ba da hidimar fasahar sadarwa na kasar Sin, ya samu ribar da ta kai kimanin Yuan triliyan 3.5, kwatankwacin dala biliyan 533, karuwar kaso 13.2 cikin 100 kan makamancin lokaci na bara. Haka kuma bangaren hidimar rumbum manyan bayanai, ya samu ribar da ta kai Yuan biliyan 153, kimanin dala biliyan 23, karuwar kaso 12.5 cikin 100 kan makamancin lokaci na bara.

Gao ya kara da cewa, tattalin arzikin yankin Asiya da Fasifik, ya dade yana dora muhimmanci kan yin hadin gwiwa a fannin tattalin arzikin yanar gizo, kuma a shirye kasar Sin take ta yi aiki da kasashen yankin, don kara cin gajiyar dake kunshi cikin fannin tattalin arzikin yanar gizo, da kara kafa ayyukan hadin gwiwa bisa akidar yin takara, da raba nasarorin da aka samu a wannan bangare tare.

Da ya juya ga sabon salon da ake fatan amincewa da shi a taron kolin hadin gwiwar tattalin arziki na kungiyar ta APEC, mataimakin ministan cinikayya na kasar Sin Wang Shouwen, ya bayyana cewa, an sanya batutuwan dake kunshe cikin tattalin arziki na yanar gizo da yayata kirkire-kirkire cikin salon hangen nesan, yayin da aka bayyana fa’idar tattalin arzikin yanar gizo, wajen tabbatar da zaman lafiya da saukaka harkokin kasuwanci yayin da ake yaki da annobar COVID-19.

Wang ya ce, kasar Sin za ta yi aiki da sauran kasashe, domin cike gibin fasahar zamani a shiyyar, da kare yadda ake amfani da matsayin kasa ta hanyar da ba ta dace ba a fannin manyan kamfanoni na zamani, da kara imani a fannin raya tattalin arzikin yanar gizo, bunkasa sabbin matakan bunkasuwa a yankin Asiya da Fasifik.

A nasa jawabin jakadan kasar Malaysia a kasar Sin, Raja Dato Nushirwan Zainal Abidin ya bayyana cewa, fasahar sadarwar zamani da bangaren watsa labarai, sun taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar Sin, yana mai tuna matsayar da ministocin kungiyar suka cimma game da tattalin arzikin yanar gizo, yayin taron ministocin kungiyar na baya-bayan nan da Malaysia ta karbi bakuncinsa.

Jakadan ya ce, tsarin fasahar sadarwar mai cike da tsaro da kowa zai iya amincewa da shi, zai iya bunkasa hadewar shiyyar da ma samar da ci gaba mai dorewa, ta yadda mambobin kungiyar za su yi musayar kwarewa, da kara fahimtar tattalin arzikin yanar gizo, ta yadda za su samar da yanayin da ya dace.

Yayin taron dandalin, shugabannin ’yan kasuwa na kasar Sin, ciki har da shugabar Didi Chuxing, madam Liu Qing, shugaban bankin kasar Sin na Bank of China, Liu Lian’ge, da shugabar kamfanin samar da kayayyakin laturoni mai suna Gree Electric Appliances madam Dong Mingzhu, sun kwatanta bayanan kayayyakin fasahar sadarwar zamani dake kamfanoninsu, inda suka bayyana tabbaci game da makomar wannan fanni.

Da yake musayar rahotonsa a taron dandalin, babban masanin tattalin arziki a hukumar kula da hannayen jarin kasa da kasa ta kasar Sin, Peng Wenshang, ya ce, tattalin arzikin yanar gizo, zai samar da tarin damammaki da za su inganta rayuwar jama’a, da harkokin kasuwanci, amma kuma tsarin yana tattare da nasa kalubale da hadurra, a don haka ya yi kira da a kara tattauna manufofin da gwamnati ta tsara game da raya tattalin arzikin yanar gizo.

Taron shugabannin kungiyar APEC na shekarar 2020 na kasar Sin, wanda CCPIT ta shirya tare da hadin gwiwar majalisar ’yan kasuwar kasa da kasa ta kasar Sin, da majalisar ’yan kasuwa kungiyar APEC dake kasar Sin, ya samu mahalarta wakilai kimanin 300 daga majalisun da shugabannin ’yan kasuwan kasar Sin, inda za su tattauna tasirin fasahar zamani, a matsayin taken bikin na bana. (Ibrahim Yaya)