logo

HAUSA

Habou Manzo: Kasar Sin tana da abubuwan koyi da yawa

2020-11-20 20:15:26 CRI

Habou Manzo: Kasar Sin tana da abubuwan koyi da yawa

A cikin shirinmu na wannan sati, Murtala Zhang ya zanta da Habou Manzo, ko kuma Aboubakar Manzo, wani dalibi dan asalin jihar Damagaram dake Jamhuriyar Nijar, wanda a yanzu haka yake karatun ilimin likitanci a jami’ar Central South dake birnin Changsha na lardin Hunan a kasar Sin.

Habou Manzo: Kasar Sin tana da abubuwan koyi da yawa

A zantawar tasu, Habou Manzo ya ce mu’amalarsa da mutanen kasar Sin tana da kyau, kuma akwai bambanci sosai tsakanin yanayin karatu na Jamhuriyar Nijar da kasar Sin. Habou Manzo ya kuma ce, yana son amfani da ilimin da ya koya a kasar Sin, musamman a fannin likitanci, domin gina kasarsa Nijar. (Murtala Zhang)