Ibrahim Issaka: Ina jin dadin karatu a Changsha!
2020-11-20 22:39:06 CRI
A cikin shirin na wannan sati, Murtala Zhang ya zanta da Ibrahim Issaka, wani dalibi dan asalin Jamhuriyar Nijar ne, wanda a yanzu haka yake karatun ilimin likitanci a jami’ar Central South dake birnin Changsha na lardin Hunan na kasar Sin.
Ibrahim wanda ya yi shekara daya da rabi yana karatu a kasar Sin, ya ce yana jin dadin karatu a Changsha, kuma bai taba gamuwa da matsalar kyamar baki a kasar ba. Ibrahim ya kuma ce ya ga babban ci gaban da kasar Sin ta samu, musamman a fannonin da suka shafi kimiyya da fasaha, abun da ya kamata kasashen Afirka su yi koyi daga kasar.
A karshe, Ibrahim ya yi kira ga matasan Afirka, su tashi tsaye su yi karatu, domin ilimi shi ne hasken rayuwa.(Murtala Zhang)