logo

HAUSA

Ba wani mataki da ya wuce hadin gwiwa idan har ana fatan warware kalubalolin duniya

2020-11-19 18:36:22 CRI

Ba wani mataki da ya wuce hadin gwiwa idan har ana fatan warware kalubalolin duniya

Tun bayan da kafofin watsa labarai na cikin gidan Amurka, suka ayyana tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden, a matsayin wanda ya lashe zaben kasar da ya gabata makwannin baya, daya daga muhimman kalamai da Mr. Biden ya yi shi ne, shan alwashin hade kan Amurkawa, da kuma tabbatar da cewa Amurka ta daina daukar abokan takarar ta a matsayin abokan gaba.

Wadannan kalamai sun kara shaida gaskiyar sassan dake yayata bukatar ci gaba da cudanyar kasa da kasa cikin lumana, da kaucewa nunawa juna kyama ko kiyayya, da kuma amincewa da manufar yin takara mai tsafta.

Kasar Sin da sauran kasashen duniya da dama, sun sha jaddada bukatar hade kan duniya, da yin aiki tare domin samar da al’ummar duniya mai makomar bai daya, tare da kauracewa ware kai, da yiwa saura matsin lamba.

A wannan gaba da tsohon mataimakin shugaban kasar Amurka, kuma shugaban kasar mai jiran gado ya sake jaddada wannan manufa, muna iya cewa gaskiya ta kara fitowa fili, dama dai “Karya fure take ba ta ’ya’ya”.

Fatan masharhanta da masana da dama, shi ne dukkanin masu ruwa da tsaki a siyasar Amurka su rungumi wadannan kalamai na Mr. Biden da muhimmanci, kasancewar hakan zai ba da damar warware tarin kalubalolin da duniya ke fuskanta a halin yanzu, musamman batutuwan da suka shafi yaki da cutar numfashi ta COVID-19, da batun sauyin yanayi, da kokarin farfado da tattalin arzikin duniya da sauransu. Dukkanin wadannan batutuwa suna da alaka da Amurka, a matsayinta na babbar kasa da ke fama da wasunsu, kuma mai fada a ji da ke iya taka rawar gani wajen warware mafi yawansu.

Ba wani mataki da ya wuce hadin gwiwa idan har ana fatan warware kalubalolin duniya

Wasu masu fashin baki na ganin daya daga dabaru mafi dacewa da ya dace Amurka ta aiwatar, wajen ba da gudummawar shawo kan matsalolin da duniya ke fuskanta, shi ne yin hadin gwiwa da kasar Sin, ta hanyar tattaunawa, da gudanar da shawarwari bisa adalci da daidaito.

Ko shakka babu, a wannan gaba da cutar numfashi ta COVID-19 ke kara haifar da mummunan tasiri a Amurka, da sassan Turai masu yawa, kuma duniya ke tunkarar karin kalubale na farfadowar tattalin arziki, kara tara abokan gaba, ba abu ne da zai haifarwa Amurka da mai ido ba.

A daya bangaren akwai kasashen nahiyar Asiya da dama, dake fatan ganin Sin da Amurkan sun hada kai da juna, ta yadda hakan zai haifar da moriya ga shiyyar, da ma sauran duniya baki daya.

Fatan dukkanin sassan duniya dai shi ne, ganin manyan kasashen duniya masu fada a ji ciki hadda Amurka, sun koma teburin shawarwari, sun yi hadin gwiwa da juna, ta yadda za a fitar da duniya daga manyan kalubale dake addabarta, har a kai ga gudu tare a tsira tare. (Saminu Hassan)