logo

HAUSA

Babban bikin bude baje kolin wasannin kankara na shekarar 2020 na Sin zai bunkasa hade sassan ci gaban wasannin kankara da na tattalin arziki da ba da hidima

2020-11-19 13:39:08 CRI

Babban bikin bude baje kolin wasannin kankara na shekarar 2020 na Sin zai bunkasa hade sassan ci gaban wasannin kankara da na tattalin arziki da ba da hidima

Masana a fannin harkokin wasanni, na bayyana babban bikin bude baje kolin wasannin kankara na shekarar 2020 na Sin, a matsayin bikin da zai bunkasa hade sassan ci gaban wasannin kankara, da na tattalin arziki, da fannin cinikayyar ba da hidima.

A bana, an bude bikin mai lakabin “2020 International Winter Sports Beijing Expo” wanda ake kira "Winter Expo" a takaice, a cibiyar nune nune ta kasa dake birnin Beijing. An dai yiwa lokacin hunturu na bana lakabin "Karfi", dusar kankara da kankara, maida "harkar cudanyar kasa da kasa, raya manasa’antu, da yayata manufofi" Manyan kudurori 3, na cimma kudurin wasannin kasa da kasa na wasannin kankara, da kuma raya ci gaban kasar Sin.

Kamar yadda kudurorin suka nuna, ta hanyar hade wadannan manufofi, ana iya cimma nasarar karfafa musaya da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, da kafa wani dandali na kasa da kasa a fannin raya wasannin kankara da na dusar kankara, da gina matsayi na daya a duniya a fannin wasannin kankara mai inganci a birnin Beijing.

A bana, bikin Winter Expo zai gudana da hadin gwiwar cibiyar kasa da kasa ta hada hadar cinikayyar ayyukan ba da hidima ta Sin ko "Service Trade Fair". Yayin da aka bude manyan bukukuwa 3 na baje koli a kasar Sin, fannin cinikayyar ayyukan hidima na Sin, shi ne irin sa na farko da ake gudanarwa a duniya. Da tallafin fannin cinikayyar ayyukan hidima da bangaren baje kolin harkokin wasanni, bikin Winter Expo na nuni ga muhimmancin da sasshen wasannin kankara ke da shi karkashin harkokin hada hadar cinikayyar ba da hidima, tare da samar da manyan damammiki ga kasa da kasa, na raya fannin wasannin kankara da na dusar kankara.

Da yammacin ranar bude baje kolin, an gudanar da bikin budewa a birnin  Beijing, inda babban mataimakin shugaban raya birnin Beijing game da wasannin Olympic Liu Jingmin ya jagoranci bikin. Kaza lika akwai manyan shugabannin masana’antu, da kwararru daga kasashen duniya da dama da suka halarci bikin ta yanar gizo, da ma wadanda suka halarta ido da ido.

Yayin bikin, shugaban kwamitin Olympic na kasa da kasa IOC Mr. Thomas Bach, ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo. Kaza lika akwai wasu karin shugabanni da suma suka gabatar da na su jawabin ta bidiyo, ciki hadda shugaban kwamitin tsare tsare na gasar Olympics ta shekarar 2022 Juan Antonio samaranch, da ministan ma’aikatar kimiyya da raya al’adu na kasar Finland Annika, da shugaban kungiyar wasannin huturu guda 2 na kasa da kasa ole, da babban sakataren gamayyar hukumomin wasannin zamiyar kankara, da jagoran kwamitin tsare tsare na wasannin lokacin hunturu na shekarar 2022 da za a yi a nan birnin Beijing, da dai sauran manyan baki ciki hadda Sara lewis.

Cikin jawabin da ya gabatar, Shugaban IOC Mr. Thomas Bach, ya ce "Ta hanyar tattaro fannonin wasannin hunturu, karkashin taken "Karfi", dusar kankara da kankara”, bikin Winter Expo ya zama dandalin musamman na yayata gudummawar da wasanni ke bayarwa a fannin farfadowa. Ya ce "Wannan baje koli yana da muhimmancin gaske, kuma mataki ne da Sin ke aiwatarwa na shirya karbar bakuncin gasar wasannin kankara ta shekarar 2022. Kaza lika Mr. Bach ya ce “Muna aiki kafada da kafada da dukkanin sassa, domin karfafa ayyukan mu, har mu kai ga zaburar da sauran sassa da ruhin wasannin Olympics, a fannin wasanni da kuma shiryawa fuskantar makoma ta gaba."

Shi kuwa a nasa jawabin, Zhang Jiandong, mataimakin magajin garin birnin Beijing, kuma babban mataimakin shugaban kwamitin shirya gasar wasannin lokacin hunturu na Beijing a shekarar 2022, kana mataimakin shugaban kungiyar raya birnin a fannin wasannin Olympic, cewa ya yi, yana fatan dukkanin masu ruwa da tsaki za su yi amfani da wannan dandali na baje kolin wasannin hunturu, wajen cimma gajiyar sassan su, su kuma yi cudanya mai zurfi da hadin gwiwa na zahiri, tare da cimma sakamako mai gamsarwa. Ya kuma yi fatan kwamitin shirya bikin baje kolin wasannin na “winter expo” zai kara zurfafa salon sa na gudanarwa, kana za a fadada harkar cinikayyar tufafin wasanni ta hanyoyi mafiya dacewa, za a kuma yi aiki kafada da kafada da sassan cikin gida da na ketare, wajen kara inganta ayyukan ofis, ta yadda za a raya ci gaban wasannin kankara da na dusar kankara masu inganci, har a kai ga raya fannonin, su zama na musamman, yayin gasar Olympic dake tafe, ta yadda gasar za ta bayar da gudummawar samar da ci gaba.

A lokaci guda kuma, akwai wasu tarukan karawa juna sani, da tarukan tallace tallace, da gabatar da manyan sanannun kwararru na kasa da kasa, da na kamfanonin da ke da wayewa a fannin, ta yadda za a tattauna dabarun inganta samar da damammakin ci gaba a sabon zamani, a fannin wasannin kankara da dusar kankara.

Baje kolin “Winter Expo” zai gudana a cibiyar nune nune ta kasa da kasa, da harabar hasumiyar kudanci ta Linglong. Za kuma a baje hajojin gida da na wajen kasar Sin kusan 20, da suka shafi wadannan wasanni, da kuma sama da salon kayayyaki 500 na gida da na wajen Sin da suka shafi wasannin. A matsayin babban sashen nune nunen, yankunan E1 da E2 na cibiyar nune nunen na da taken “wasannin Olympic na kankara na hukumomin kasa da kasa”, da “sanannun kayayyakin kasa da kasa na wasannin kankara da dusar kankara”, da “Cinikayyar kasa da kasa ta harkokin hidima na wasannin kankara, da dusar kankara da fasahohin su”,.

Sai kuma “Fasahohin wasannin kankara da dusar kankara da wuraren baje kolin kayayyakin yin wasan, da nune nunen kirkire kirkire kasa da kasa na hukumomin shirya wasannin, da kamfanoni mafiya shahara a fannin wasannin kankara da dusar kankara, da cibiyoyin su ta siga mafi kyawu.

Yankunan kudanci na A, B, C da harabar hasumiyar linglong mai alamta gasar Olympic, da ayyukan zamiyar kankara da wurin ginin filin, da fasahohi, da kayan aiki, da wuraren aiki na rufaffen wuri da na waje na wasan kankara da dusar kankara na fannin yawan bude ido a lokacin hunturu, duka dai masu nasaba da rukunin larduna da birane. Sai kuma fannin horo na wasannin kankara da dudar kankara, da bikin kalankuwar wasannin da hadin gwiwar kafafen watsa bayanai, don fadakar da al’umma game da su, da hanyoyin sayen hajoji, da hidimomin sayen su, kamar na baje koli, da jawo hankulan masu sha’awar wasannin hunturu na kasa da kasa, su baje kolin abubuwan da suka kayatar da su, da yayata wasannin kankara.

An fara gudanar da baje kolin “Winter Expo” a birnin Beijing tun daga shekarar 2016, inda ake yin shi a duk shekara. A bana kuma ake gudanar da bikin a karo na 5. Bisa alkawarin da birnin na Beijing ya yi ga sassan kasa da kasa, lokacin da yake neman amincewar ya karbi bakuncin gasar Olympic ta lokacin hunturu na shekarar 2022, “Winter Expo”, ya zamo dama ta taimakawa gaggauta ci gaban wasannin hunturu na kasar Sin, da ma kamfanoni masu ruwa da tsaki a wasannin kankara da dusar kankara, da fafada tasirin su a duniya kamar yadda ake gani yau da kullum.

Za a gudanar da “Winter Expo” a tsawon kwanaki 5. Zai kuma hade sassan albarkatun wasannin kankara, da na dusar kankara na kasa da kasa, da karfafa musaya ta kasa da kasa da hadin gwiwa, da bunkasa ci gaba mai dorewa cikin lumana a fannin wasannin kankara da dusar kankara na Sin, zai kuma tanadar da karfin cimma nasarar karbar bakuncin gasar wasannin Olympics na hunturu wanda ke tafe karkashin tsarin nune nune, da taken wasu dandali da za a gudanar, da shirye shiryen da wasu masana’antu masu ruwa da tsaki a fannin za su aiwatar.