logo

HAUSA

Babban taron intanet na duniya ya bukaci samar da makoma ta bai daya a fannin intanet

2020-11-19 10:30:47 CRI

Mashirya babban taron intanet na duniya, sun gabatar da wani daftarin shiri game da hadin hannu wajen gina al’umma mai makoma ta bai daya a fannin intanet, inda suka yi kira da a inganta kirkire-kirkiren zamani da gaggauta samar da kayyakin samar da bayanai a duniya.

Daftarin ya ce annobar COVID-19 ta bayyana bukatar dake akwai na hada hannu a bangaren intanet, inda ya yi kira da hadin kai da tabbatar da adalci da tsare gaskiya da moriyar juna.

A cewar daftarin shirin, ya kamata a yi kokarin hada gwiwa da tattaunawa a matakan kasa da yanki da bangarori daban-daban da ma duniya baki daya, a wani yunkuri na inganta aminci tsakanin kasashe a fannin intanet.

Sauran shawarwarin da daftarin ya gabatar sun hada da taimako da tallafawa rukunoni masu rauni a bangaren, domin taimaka musu inganta basirarsu da kuma kawar da abubuwan dake tarnaki ga shiga kasuwanni domin saukaka cinikayya tsakanin kasa da kasa. (Fa’iza Mustapha)