logo

HAUSA

Xi ya gabatar da jawabi a taron shugabannin Apec

2020-11-19 16:26:38 CRI

Xi ya gabatar da jawabi a taron shugabannin Apec

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron shawarwarin shugabannin masana’antu da cinikayya na kungiyar APEC ta kafar bidiyo tare da gabatar da jawabi, inda ya yi nuni da cewa, a wannan shekarar da muke ciki, kasar Sin maimakon ta dakatar da bude kofarta ga kasashen waje, ta gabatar da karin wasu manufofi na bude kofarta ga kasashe daban daban. 

Ya ce,“A don haka, akwai bukatar kasashe su taimakawa juna yayin da suke cikin mawuyacin hali, su rungumi akidar hadin gwiwa, da karfafa munafar tuntubar juna, da zurfafa hadin gwiwar kasa da kasa kan yaki da COVID-19, da gina tsarin tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa, da kokarin ganin bayan annobar nan da nan, da samun dawamamman ci gaba mai dorewa, da ci gaban tattalin arzikin duniya da zai kunshi kowa da kowa.”

Ya ce bude kofa yana daga cikin manufofin kasar na samun ci gaba, yayin da rufe kofa babu abin da zai haifar sai koma baya. A don haka kasar Sin ta riga ta shiga tsarin tattalin arzikin duniya da tsarin kasa da kasa. Sin ba za ta fice daga harkokin kasa da kasa ba, kuma ba za ta rufe kofarta da ma kin amincewa da sauran kasashe ba.

Xi Jinping ya yi nuni da cewa, Sin za ta kara kokari tare da gabatar da karin matakai, don kawar da abubuwan dake kawo cikas ga raya tsarin tafiyar da harkokin kasa. Haka kuma kasar Sin tana ba da muhimmanci ga aikin kirkire-kirkire wajen samun ci gaba, matakin da ya dade yana ba da taimako wajen raya tattalin arzikin Sin. Bisa sabon tsarin samun bunkasuwa na yanzu, kasuwar Sin za ta kara taka muhimmiyar rawa don kara biya bukatun kasashen duniya.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana cewa, kasar Sin za ta shiga a dama da ita wajen rabon nauye-nauye da shiga cikin tsarin samar da kayayyaki na duniya, da kuma fadada musaya da hadin gwiwa da sauran kasashe.

Ya kara da cewa, kasar Sin za ta yi maraba da dukkan kasashe da yankuna da kamfanonin dake sha’awar hada gwiwa da ita. Ya kuma jaddada cewa, akwai bukatar a ci gaba da inganta dunkulewar tattalin arzikin yankin, da gaggauta kirkire-kirkiren ci gaba, da hada yankuna da cimma dawwamammen ci gaba na bai daya, da kokarin cimma burika daki-daki tare da samar da moriya ga al’ummun yankin Asiya da Fasifik.

A cewarsa, zurfafa hadin gwiwa ta fuskar ci gaba da tattalin arzikin yankin Asiya da Fasifik zai ci gaba da bayyana karin kuzari.

Ya ce,“Za a gaba bayan wannan annoba, kuma nasara na nan tafe. A don haka ya kamata mu hada hannu, mu kasance tare da ma taimakawa juna ko ta halin kaka, mu ci gaba da bude kofa da yin hadin gwiwa, ci gaba da kai komo a ciki da wajen kasashenmu, mu samar da makoma mai haske ga yankin Asiya da Fasifik da ma duniya baki daya.” (Ibrahim Yaya)