logo

HAUSA

Xi Jinping ya gabatar da jawabi yayin taron shugabannin kasashen kungiyar BRICS karo na 12

2020-11-18 13:23:17 CRI

Taron shugabannin kasashen kungiyar BRICS karo na 12 da shugaban Rasha, kuma shugaban kungiyar a wannan karon wato Vladimir Putin ya jagoranta, ya samu halartar shugaban kasar Sin, Xi Jinping da shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa da Firaministan Indiya Narendra Modi da kuma shugaban Brazil Fabio Bossonaro.

A jawabin da ya gabatar yayin taron, shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya ce yanayin barkewar annoba a karni na 21 da sauye-sauyen da aka samu a karnin da ya gabata na hade da juna, inda ya ce duniya ta fuskanci manyan sauye-sauye. Kuma al’ummun duniya na fuskantar annoba mafi muni, sannan tattalin arzikin duniya ya shiga mawuyacin halin da bai taba shiga ba tun bayan wanda ya shiga a shekarun 1930, ya na mai cewa, taron na shugbannin BRICS na musammam ne da ya zo a lokaci mai muhimmanci.

A jawabin nasa, shugaba Xi Jinping ya tabo wasu muhimman batutuwan jan hankali ga kasashen na kungiyar BRICS. A cewarsa:“mun yi ammana cewa taken lokacin zaman lafiya da ci gaba bai sauya ba, kuma tabbatar da  daidaiton iko a duniya da dunkulewar tattalin arziki abubuwa ne da ba za su sauya ba. Ya kamata mu kula da rayuwar jama’armu da daukaka burin gina al’umma mai makoma ta bai daya da kuma bada gudunmuwarmu wajen daukar kwararan matakan kyautata yanayin duniya”

Abu na farko cikin batutuwan da ya tabo shi ne, daukaka dangantakar kasa da kasa da kare zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya. Ya ce yayin da ake fuskantar abubuwan da suka hada da aiwatar da ra’ayin kashin kai da kuma huldar kasa da kasa, ga kuma adalci da babakere a daya bangaren, ya kamata kasashen BRICS su rungumi gaskiya da adalci da daukaka huldar kasa da kasa karkashin tsarin MDD da kiyaye ka’idojin majalisar da ma dokokin kasa da kasa.

Ya ce abu na biyu shi ne, nacewa ga hadin kai da hadin gwiwa domin shawo kan kalubalen annobar COVID-19. Ya ce akwai bukatar karfafa hadin gwiwar kasa da kasa wajen kandagarki da takaita yaduwar annobar da kuma mara baya ga muhimmiyar rawar da shugabancin hukumar lafiya ta duniya WHO ke takawa. A cewarsa, a shirye Sin take ta duba yuwuwar samar da alluran riga kafi ga kasashen BRICS dake bukata. Kuma za su inganta kafa cibiyoyin bincike da samar da riga kafi a kasashen BRICS, yana mai cewa, Sin na gabatar da bukatar gudanar da taron karawa juna sani kan magungunan gargajiya domin lalubo irin rawar da za su taka wajen kandagarki da magance COVID-19.

Na uku, shugaba Xi ya ce akwai bukatar kasashen BRICS su rungumi tsarin gaskiya da kirkire-kirkire domin inganta farfadowar tattalin arzikin duniya. Ya ce za su karfafa manufofin da suka shafi harkokin tattalin arziki da inganta aiwatar da shirin saukaka zirga-zirgar mutane da kayayyaki tsakanin iyakokin kasa da kasa da tabbatar da tsarin samar da kayayyaki ya gudana cikin aminci ba tare da wata tangarda ba.

Bugu da kari, shugaban na kasar Sin ya ce akwai bukatar kasashen su bada muhimmanci ga rayuwar jama’arsu da inganta muradun ci gaba masu dorewa na duniya. Ya ce za su sanya batun aiwatar da ajandar ci gaba mai dorewa da ake son cimmawa zuwa 2030 a matsayin jigon hadin gwiwar neman ci gaba na kasa da kasa, da bada muhimmanci ga aikin kawar da talauci da ware karin albarkatu ga shirin kawar da talauci da samar da ilimi da kiwon lafiya da ababen more rayuwa da sauran fannoni.

A cewarsa, abu ne biyar shi ne, kare muhalli da rage sinadarin carbon domin kyautata alakar dake tsakanin muhalli da dan adam. Ya ce za su aiwatar da yarjejeniyar sauyin yanayi ta birnin Paris, da kiyaye ka’idojin bai daya da sauke mabanbantan nauyin dake wuyansu tare da samar da karin taimako ga kasashe masu tasowa. Ya ce kasar Sin za ta kara yawan gudunmuwar da take bayarwa. Sannan, ta sanar da kwararan manufofi da matakan kai wa koli wajen fitar da sinadarin carbon zuwa 2030 tare kuma da cimma burin daina fitarwa baki daya zuwa 2060.

Shugaban na kasar Sin ya jaddada cewa, kasarsa za ta bude sabon babin gina kasa mai tsarin gurguzu na zamani, yana mai cewa, za ta kai wani sabon matakin ci gaba ta hanyar kimiyya da kuma aiwatar da sabon tsarin da taswirar ci gaba.

Ya ce “ dukkan mu muna cikin yanayi guda. Idan muka shiga mawuyacin hali, abu mafi muhimmanci garemu shi ne ci gaba da bin tafarkin da ya dace, mu nazarci yanayin, mu kuma hada hannu don samun ci gaba domin kyautata makomarmu”.

Karkashin taken “zurfafa hadin gwiwa domin kwanciyar hankalin duniya da tsaro na bai daya da kuma sabon ci gaba” shugabannin kasashen 5 sun tattauna kan hanyoyin yaki da COVID-19 da samar da tsarin raya kungiyar BRICS tare da musayar ra’ayi mai zurfi da cimma matsaya guda kan hadin gwiwar kungiyar da kuma halin da duniya ke ciki.

Yayin da ake fuskantar annobar COVID-19, shugabannin sun ce akwai bukatar hadin gwiwa da taimakon juna tsakanin kasashen biyar, da karfafa hadin gwiwa kan samar da magunguna da alluran riga kafi da mara baya ga hukumar WHO a aikin da take yi da adawa da siyasantar da batun annobar, da tabbatar da aminci a bangaren samar da kayayyaki, da inganta farfadowar tattalin arzikin duniya da bunkasarsa. Har ila yau, sun ce za su zurfafa hadin gwiwarsu a fannin cinikayya, da zuba jari, da tattalin arzikin zamani, da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, da makamashi, da sauyin yanayi.

Baya ga haka, sun ce, ya kamata su karfafa hadin gwiwa a fannin siyasa da tsaro, ciki har da yaki da ta’addanci, da cin hanci, da tsaron sararin samaniya, da kafar intanet, da girmama cikakken ‘yanci da iko da tsaron kasashe, da kuma kokarin warware rikici cikin lumana.

Haka zalika, za su fadada musaya da hadin gwiwa da abota tsakanin jama’arsu. Sun kuma amince su ci gaba da tuntubar juna kan muhimman batutuwan da suka shafi kasa da kasa da yankunansu, da inganta tsarin shugabanci, da huldar kasa da kasa, da kiyaye dokokin MDD da kuma kokarin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya ga bil adama.

Shugabannin kasashen 5 na Brazil da Rasha da India da Sin da Afrika ta kudu, sun kuma saurari rahoton ayyukan kowannensu ta fuskar tsarukan kungiyar. (Fa’iza Mustapha)