logo

HAUSA

Yawan wadanda suka kamu da COVID-19 a Najeriya ya zarce dubu 65

2020-11-17 10:07:06 CRI

Rahotanni daga Najeriya na cewa, yawan wadanda suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 ya kai dubu 65 da 148, yayin da ake fargabar sake bullar cutar a karo na biyu, duk da cewa wadanda ke kamuwa da cutar a duk rana ba ya karuwa cikin sauri.

Cibiyar kandagarki da hana yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta tabbatar a karshen mako cewa, an samu sabbin mutane 152 da suka kamu da COVID-19 a kasar dake yammacin Afirka, abin ya kai adadin wadanda suka kamu da cutar a kasar zuwa 65,148.

An dai ba da rahoton sabbin mutanen da suka kamu da cutar ce a jihohi 7 na kasar da kuma Abuja, babban birnin kasar, sai dai ba a samu rahoton wadanda suka mutu sanadiyar cutar ba.

Koda yake alkaluman da cibiyar NCDC ta fitar sun nuna cewa, ya zuwa yanzu, yawan mutanen da cutar ta halaka ya kai 1,163 baya ga mutane 61,073 da suka warke daga cutar.

A ranar 27 ga watan Fabrairu, Najeriya ta samu yawan wadanda suka kamu da cutar a Lagos wadda ke zama cibiyar kasuwancin kasar. Alkaluman NCDC sun nuna cewa, kasar Najeriya ta fuskanci adadi mafi yawa na wadanda cutar ta kama tsakanin farkon watan Yuni da karshen watan Agusta, inda cutar ta kama mutane da suka kai 790 a ranar 1 ga watan Yuli. Sai dai yawan alkaluman wadanda ke kamuwa da cutar a duk rana sun yi kasa, tun a karshen watan Agusta, inda galibi a rana ake samun kasa da mutane 200 dake kamuwa da cutar.

A ranar 5 ga watan Nuwamba, ministan lafiya na kasar Osagie Ehanire, ya bayyana damuwa kan yiwuwar sake bullar cutar a karo na biyu, wanda ya ce babu tantama, don haka ya yi kira da a kara inganta tsarin kiwon lafiyar kasar.

Sai dai kuma, Ehanire ya ce, an riga an yiwa tsarin kiwon lafiyar kasar garambawul. Yana mai cewa, kasancewar Lagos babbar mashigar kasar ta kasa da kasa, kana birni mai hada-hada, gami da hadarin sake yiwuwar bullar cutar a karo na biyu, ya fuskanci ninkin tasiri annobar, ga kuma bore baya-bayan nan game da kin jinin cin zalin ‘yan sanda a Najeriya da aka gudanar, abubuwan da suka sake auna karfin tsari da cibiyoyin kiwon lafiyar kasar.

A ranar 4 ga watan Nuwanba kuma, sakataren gwamnatin Tarayyar Najeriya Boss Mustapha, shi ma ya yi bayanin cewa, kimanin kaso 65 cikin 100 na ‘yan najeriya dake dawo wa cikin kasar daga ketare, ba sa martaba ka’idojin gwaji na cutar a baya-bayan nan.

Ita ma gwamnatin jihar Lagos, ta ja kunnen mazauna jihar cewa, ci gaba da rashin mutunta matakan yaki da cutar da na kariya, ka iya haifar da bullar cutar a karo na biyu a jihar.

A wata zantawa da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a baya-bayan nan, darektan kiwon lafiya na gaggawa, shirye-shirye da mayar da martani a cibiyar NCDC, John Oladejo, ya bayyana cewa, hukumar kula da lafiyar jama’a tana aiki tukuru, don ganin ba a samu bullar cutar a karo na biyu ba.

Sai dai ya ce,idan ba a manta ba, kwanakin baya, an shirya zanga-zanga, kuma mutane da dama sun hallara. Idan daya daga cikinsu yana da COVID-19, to hakan na nufin cutar za ta bazu a ko’ina.

A saboda haka, ya ce, cibiyar NCDC ta kara kaimi kan wannan lamari, ta kuma horas da ma’aikatan lafiyar al’umma masu aikin sa-kai, don tabbatar da cewa, idan aka gano masu alamomin cutar, za su yi hanzarin fito da su, a yi musu gwaji a kuma ba su magani.

Jami’in ya ce, daga cikin matakan da aka riga aka dauka don hana sake bullar cutar a karo biyu sune, cibiyar za ta tabbatar da cewa, an ilimantar da al’umma game da sanya marufin baki da hanci a duk lokacin da suke halartar taruka, da ba da tazara da kuma wanke hannaye da sabulu akai-akai bayan sun taba gurbataccen abu ko a’a

Daga karshe ya ce, yanzu haka sun baza kwararru. Baya ga yadda suke aiki ba dare ba rana don tabbatar da cewa, cutar ba ta sake bulla a karo na biyu ba a kasar.(Ibrahim)