logo

HAUSA

Kasashen kungiyar APEC sun kuduri niyyar farfado da tattalin arziki daga tasirin COVID-19

2020-11-17 13:27:25 CRI

Kasashe mambobin kungiyar hadin gwiwa ta yankin Asiya da Fasifik (APEC), sun jaddada kudurinsu na gudanar da ciniki da zuba jari cikin ‘yanci tare da kara himmantuwa wajen farfado da tattalin arzikin yankin daga mummunan tasirin annobar COVID-19.

Da yake jawabi yayin taron ministocin kasashen APEC da aka yi ta kafar bidiyo a jiya, ministan kula da cinikayya da kasashen waje na kasar Malaysia, Mohamed Azmin Ali, wanda ya jagoranci taron, ya nanata bukatar kasashe mambobin kungiyar, su ci gaba da adawa da kariyar cinikayya tare da karfafa tsarin cinikayya tsakanin kasa da kasa.

Ya ce kasashen APEC sun inganta ajandar ciniki da zuba jari a yankin, yayin da gudanar da cinikayya da zuba jari cikin ‘yanci ya zama wajibi a lokacin da ake cikin mawuyacin hali.

Ya ce wannan na nanata kudurin yankin Asiya da Fasifik na ci gaba da adawa da duk wani nau’i na kariyar cinikayya.

Taron ministocin na zuwa ne gabanin taron shugabannin kasashen kungiyar, wanda zai gudana ta kafar bidiyo a ranar 20 ga wata, inda aka sa ran za a amincewa a hukumance, da burin da kungiyar ke da shi bayan shekarar 2020.

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da aka fitar bayan taron, ministocin sun ce za su hada hannu wajen saukaka jigilar kayayyaki da hidimomi tsakanin iyakoki ba tare da yin cikas ga kokarin dakile yaduwar cutar COVID-19 ba, da kuma lalubo hanyoyin saukaka zirga-zirgar mutane tsakanin iyakokin. (Fa’iza Mustapha)