logo

HAUSA

Jami’in Sin: Kulla yarjejeniyar RCEP zai taimakawa ciniki cikin ‘yanci a duniya

2020-11-16 14:03:48 CRI

A jiya Lahadi, an yi bikin sa hannu kan yarjejeniyar huldar abokai ta fannin tattalin arziki ta shiyyar gabashin Asiya da tekun Pasific (RCEP), inda ministocin kasuwanci na wasu kasashe 15 suka sa hannu kan yarjejeniyar, cikin har da wakilin kasar Sin.

Da ma wasu kasashe 10 dake cikin kungiyar kudu maso gabashin Asiya sun kaddamar da shirin yarjejeniyar RCEP, inda suka gayyaci kasashen Sin, da Japan, da Koriya ta Kudu, da Australiya, da New Zealand, da Indiya, don a bullo da wani tsari na samar da ‘yancin ciniki, a shiyyar da suke ciki.

A watan Nuwanban shekarar 2012 ne, aka kaddamar da tattaunawa game da yarjejeniyar. Ya zuwa bara, wasu kasashe 15 sun kammala tattaunawa, karkashin laimar yarjejeniyar. Ban da kasar Indiya, wadda ba ta shiga yarjejeniyar ba sakamakon wasu batutuwan da ba ta daidaita su ba tukuna. Duk da haka, wasu alkaluman da aka fitar a shekarar 2018 sun nuna cewa, yawan al’ummun kasashe 15 da suka amince da yarjejeniyar RCEP, ya kai biliyan 2.3, kwatankwacin kashi 30% na daukacin al’ummar duniya. Kana jimillar GDPn su ta zarce dalar Amurka triliyan 25.

A nasa ra’ayi, mista Wang Shouwen, mataimakin ministan kasuwancin kasar Sin, ya ce yarjejeniyar RCEP tana da ma’ana sosai, musamman ma a fannin ciniki cikin ‘yanci. Ya ce,

“A nan gaba, tsakanin mambobin kasashen da suka kulla yarjejeniyar, za a kawar da harajin kwastam da ya shafi kashi 90% na kayayyakin da ake cinikinsu. Sa’an nan a fannin cinikin hidimomi, za su kara bude kofa a tsakaninsu, wanda zai fi tsarin na yanzu na hukumar ciniki ta duniya WTO. Ban da wannan kuma za a samar da karin damammaki ga masu neman zuba jari na kasashen waje.”

A cikin kasashen da suka sa hannu kan yarjejeniyar RCEP, akwai kasashe masu ci gaban tattalin arziki, da wadanda tattalin arzikinsu ke tasowa, har ma da wasu da suke fama da koma bayan tattalin arziki. Don haka yayin da aka tsara yarjejeniyar, an lura da bambancin dake tsakaninsu sosai, don tabbatar da daidaiton moriya a tsakaninsu. Ban da haka, an tsara wasu ayyukan da suka shafi kanana da matsakaitan kamfanoni, da raya tattalin arziki, musamman ma domin taimakawa kasashe masu tasowa samun ci gaba.

Mista Wang ya kara da cewa, yarjejeniyar RCEP za ta aza harsashi ga aikin kyautata ciniki cikin ‘yanci, musamman ma tsakanin kasashen Sin, da Japan, da Koriya ta Kudu.

“Da ma babu yarjejeniyar ciniki cikin ‘yanci a tsakanin Sin da Japan, ko kuma a tsakanin Japan da Koriya ta Kudu. Sai dai yanzu albarkacin yarjejeniyar RCEP, mun kulla huldar ciniki cikin ‘yanci tsakanin gabobin 3. Wannan batu na da ma’ana matuka. ”

Ta la’akari da yadda yawan al’umma da tattalin arziki, da ciniki da ake samu a kasashe 15 da suka kulla yarjejeniyar RCEP, dukkansu sun kai kashi 30% na jimillar daukacin duniya, abun da ya sa kulla yarjejeniyar ke alamta dunkulewar kashi 1 cikin kashi 3 na tattalin arzikin duniya zuwa wata babbar hadaddiyar kasuwa. A ganin Wang Shouwen, batun ya nuna babban ci gaban da aka samu a fannin dunkulewar tattalin arziki shiyyar gabashin Asiya. A cewar Wang,

“A nahiyar Tuwai, akwai wata babbar kasuwa ta kungiyar tarayyar Turai EU, kana a arewacin nahiyar Amurka, akwai yarjejeniyar ciniki cikin ‘yanci ta kasashen Amurka, da Kanada, da kuma Mexico. A wannan karo, a shiyyar gabashin Asiya, mun samu wannan tsarin da ya hada tattalin arzikin kasashe 15 waje guda, wanda zai ba da damar rage harajin kwastam, da samar da karin ‘yanci a fannin cinikin hidimomi, da zuba jari. Lamarin da zai haifar da alfanu ga yunkurin raya tattalin arzikin shiyyar.”

Mista Wang ya kara da cewa, kulla yarjejeniyar RCEP shi ma zai taimakawa tattalin arzikin duniya samun farfadowa daga tasirin cutar COVID-19. (Bello Wang)