logo

HAUSA

Menene sirrin bunkasuwar ilmin kasar Sin?

2020-11-16 17:05:52 CRI

Menene sirrin bunkasuwar ilmin kasar Sin?

Lallai wani kaya sai amale, in ji ’yan magana. Ko shakka babu, ilmi shi ne gishirin zaman rayuwa, kuma shi ne tubalin ginin ci gaban duk wata al’umma. Bisa la’akari da alfanun da wannan muhimmin fanni ke da shi ya sa mahukuntan kasar Sin ke mayar da hankali sosai wajen daukar kwararan matakan bunkasa fannin ilmin kasar. Wasu alkaluma da mahukuntan kasar suka fitar a kwanan nan ya nuna cewa, a shekarar 2019, yawan kudaden da kasar Sin ta zuba a fannin ilmin kasar ya zarce kudin kasar yuan triliyan 5 kwatankwacin dala biliyan 748.8.

Menene sirrin bunkasuwar ilmin kasar Sin?

Alkaluman sun nuna cewa, adadin kudaden yau da kullum da ake kashewa a fannin ilmin kasar Sin ya zarce kashi 4 bisa 100 na yawan GDPn kasar na shekaru takwas a jere tun daga shekarar 2012. Hakika, matakan da gwamnatocin kasar Sin ke dauka na tsayawa tsayin daka wajen bunkasa fannin ilmin kasar ya taimaka mata wajen samun gagarumin cigaba musamman a fannonin bincike, da fasahohin zamani, da cigaban kimiyya, da fannin kirkire kirkire wadanda su ne sirrin manyan nasarorin da kasar ta samu a cikin kankanin lokaci. (Ahmad Fagam)