logo

HAUSA

Baki da rawayen kogi

2020-11-16 16:49:17 CRI

 

Kasar Sin na daya cikin kasashen da suka fi yawan koguna a duniya. Sai dai daga cikin dimbin kogunan, akwai wani da al’ummar kasar suke daukarsa a matsayin uwa, a sakamakon yadda kaka da kakaninsu suka fara rayuwa a shiyyar da kogin ya ratsa, inda kuma suka fara samun wayewar kansu, kogin da ake kira rawayen kogi, ko kuma yellow river a Turance.

Baki da rawayen kogi

Rawayen kogin ya taso ne daga tsakiyar lardin Qinghai na kasar, sa’an nan ya yi ta malala har ya ratsa wasu larduna da jihohi 9, kafin daga bisani ya shiga cikin teku. Tsawon kogin ya kai kilomita 5500, abin da ya sa ya zama babban kogi na biyu na kasar Sin.

Birnin Lanzhou, hedkwatar lardin Gausu na kasar Sin, ya kasance birnin da rawayen kogi ya ratsa. To, shin ko ta yaya rawayen kogin ya kasance, kuma shin kuma ko yaya birnin Lanzhou yake? A cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku labaran wasu baki da ke zaune a birnin na Lanzhou, don su ba ku amsar tambayoyin.

Rich Pluta,dan shekaru 46 da haihuwa, wanda ya zo daga jihar New York ta kasar Amurka, kawo yanzu ya shafe tsawon shekaru biyar yana rayuwa a birnin. A lokacin da yake da shekaru 6 da haihuwa, wani littafin da ya karanta dangane da wasan Kungfu ya ba shi sha’awa matuka, bayan ya girma, tarihin kasar Sin da al’adun kasar sun jawo hankalinsa sosai. Ya ce,“Lokacin da nake dalibta, na sadu da dalibai da dama da suka zo daga kasar Sin, kuma na ji dadin kasancewa tare da su sosai. Sun koya mini wasan kwallon tebur da sarrafa abincin Sinawa, sun kuma bayyana mini al’adun da suka shafi bikin bazara da sauransu. Na karu sosai daga gare su.”

Baki da rawayen kogi

Kawo yanzu Rich Pluta ya shafe kimanin shekaru 15 yana rayuwa a kasar Sin, har ma ya ziyarci biranen kasar sama da 30, kafin daga bisani ya je birnin Lanzhou ya zauna, birnin da uwargidansa ta fito, kuma kusan nan take, ya fara kaunar wannan birni da rawayen kogi ya ratsa. Ya ce,“Lokacin da na fara zuwa birnin Lanzhou, na lura da cewa, birni ne mai al’adu iri daban daban. Misali, lokacin da nake yawo a kan hanya, na kan sadu da mutanen sanye da tufafin kabilu daban daban, wato al’ummomi na cudanya a nan birnin tare da al’adunsu iri daban daban. A birnin Lanzhou, ‘yan kabilu daban daban na kiyaye al’adunsu na gargajiya, abin da ya burge ni kwarai da gaske.”

Birnin Lanzhou shi ne hedkwatar lardin Gansu na kasar Sin, kana hedkwata daya kacal da rawayen kogin ya ratsa a cikin hedkwatocin larduna daban daban na kasar. A game da yadda birnin ya ba shi sha’awa, ya ce,“To, daga karshe na ga rawayen kogi. Idan kuna sha’awar tarihin kasar Sin kama ta, to, tabbas kun san ma’anar rawayen kogi ga mazauna gabobinsa. A baya, kogin yana samar da ruwa ga mazaunansa, a yayin da yake kuma taka muhimmiyar rawa ta fannin zirga zirgarsu. Ya zuwa yanzu kuma, ba za a iya raba rawar da yake takawa ba, kasancewarsa ya sa kaimi ga bunkasuwar harkokin yawon shakatawa a wurin.”

A cikin ‘yan shekarun baya, mahukunta wurin sun yi ta kokarin gyara yanayin muhallin kogin, matakin da ya sa shiyyar da kogin ya ratsa ta kara ni’ima. Liu Tianlang ya ce,“A gani na, tattalin arzikin shiyyar ya bunkasa, a sakamakon yadda aka yi ta bunkasa harkokin yawon shakatawa da suka shafi rawayen kogi, abin farin ciki ne gare ni, da mai dakina, da ma diyarmu. Musamman ma a lokacin damina, mu kan yi yawo a gabar kogin, mu motsa jiki, kuma mu shakata.”

Baki da rawayen kogi

Yau kimanin shekaru 11 da suka wuce, malama Pronkina Olga ta zo birnin Lanzhou har ta zauna, kuma, daga nan ne rayuwarta ta hade da birnin.

“Suna na Pronkina Olga, kuma na zo ne daga birnin Penzenskaya Oblast na kasar Rasha, yanzu ina aikin fassara Rashanci da kuma nazarin al’adun kasar Sin.”

Malama Pronkina ta iya Sinanci sosai, amma farkon zuwanta birnin a shekarar 2009, ko kadan ba ta iya ba. Ta ce, birnin Lanzhou ya fara burge ta ne da rawayen kogin da ta karanta a littafi, a lokacin da take makarantar midil. Ta ce,“Da nake cikin shekara ta biyu a makarantar midil, mun karanta wasu sanannun koguna biyu na kasar Sin a littafinmu na koyon yanayin kasa, daya shi ne rawayen kogi, dayan kuma ya kasance kogin Yangtze. A lokacin na tambaya, me ya sa ake kira shi rawayen kogin, malaminmu ya ce, sabo da launin kogin ya kasance rawaye. Da na zo nan na ga kogin, lalle na tuna da darrusan da muka koya har na ji tamkar na koma yarantaka.”

Malama Pronkina Olga ta fara soyayya da birnin Lanzhou sannu a hankali, musamman ma fasahohin al’ummar wurin iri iri, wadanda suka janyo hankalinta sosai, tana mai cewa,“Ina matukar sha’awar fasahohin gargajiya na al’ummar Sinawa, misali fasahar yanka takarda da rubutun hannu da zane-zane, kasancewar lardin Gansu yana da kabilu da dama, shi ya sa fasahohin gargajiya ma suna da yawa ga kabilu daban daban.”

Daga baya, malamar tana son kara nazari da kuma fahimtar al’adun da ke tattare da fasahohin. Don haka, ta fara koyon yaren Sinanci.“Ya zama dole a koyi harshe, da ka iya harshe za ka iya gano al’adun kasar. Misali fasahar yanka takarda, ba kawai ta kasance fasaha bace kadai, tana kuma da dimbin ma’ana. Amma ba za a fahimci hakan ba idan ba a koyi harshen ba.”

Baki da rawayen kogi

A yayin da take koyar da harshen Rashanci a wata jami’ar da ke birnin Lanzhou, malamar ta yi amfani da duk wata damar da ta gano, wajen koyon yaren Sinanci. Bayan da ta iya yaren, sai ta kama aikin fassara, kuma kwarewarta wajen iya Sinanci ma sai ta dinga kyautata, matakin da kuma ya sa ta kara fahimtar kasar Sin.

A cikin ‘yan shekarun da suka wuce, malamar ta fassara dimbin littattafan da suka shafi tarihi da al’adu na kasar Sin. A karshen bara, ta kuma samu lambar yabo ta Dunhuang da gwamnatin lardin Gansu ta ba ta, don martaba gudummawar da ta bayar a matsayin ta na bakuwa. A ganinta, hakan ya samu ne a sakamakon yadda take matukar kishin birnin. Ta ce,“Birnin Lanzhou ya kasance garinmu na biyu, nan gida na ne.”

Baki da rawayen kogi

A yayin bullar annobar Covid-19 a wannan shekara, malama Pronkina Olga ta tsaya a birnin Lanzhou tare da iyalanta, don ta hada kai da aminanta Sinawa wajen yakar annobar.

Yanzu an samu nasarar shawo kan cutar a kasar Sin, kuma malamar ta kan tafi gabar rawayen kogi tare da dalibanta, inda ta kan yi hira da su game da kasarta mahaifa, ta ce, a can kasar ma, akwai wani kogin da al’umma suke daukar shi a matsayin uwa.“Na san ana daukar rawayen kogi a matsayin uwa a kasar Sin, wato kasar Sin ‘ya ce ga wannan kogi. Can a kasarmu Rasha ma, akwai wani kogin da muke daukarsa a matsayin uwa, wato kogin Volga, wanda shi ma ya ratsa jihohi da birane da dama. Lokacin da nake kewar gida, na kan je gabar rawayen kogi tare da dalibaina, inda muke cin gasashen nama na kasarmu Rasha, mu yi hira kuma mu yi dariya.”