logo

HAUSA

AfCFTA Na Alamta Makoma Mai Haske A Najeriya

2020-11-15 18:21:07 CRI

AfCFTA Na Alamta Makoma Mai Haske A Najeriya

 

Kwanakin baya, gwamnatin tarayyar Najeriya ta tabbatar da shigar kasar cikin yarjejeniyar AfCFTA, dake mai da nahiyar Afirka a matsayin wani yanki mai cikakken ’yancin ciniki. Wannan labari ya janyo hankalin jama’ar kasar, wadanda suke fatan ganin wannan dama za ta haifar da ci gaba ga kasar Najeriya, gami da daukacin nahiyar Afirka. Babu shakka, wannan hadin gwiwar da ake yi a nahiyar Afirka, za ta samar da dimbin damammaki na raya kasa da al’umma a kasashen Afirka, ciki har da Najeriya.

Masu iya magana na cewa, ba kullum ake kwana a gado ba. Wannan magana haka take, saboda idan mun nazarci abubuwan dake faruwa a duniya, za mu gano cewa abubuwa na canzawa babu kakkautawa. Saboda haka, yadda ake rungumar yadda al’amura ke sauyawa, gami da karbar sabuwar manufa, su kansu, babban ci gaba ne.

A kwanakin baya, a kasar Sin, an yi bikin murnar cika shekaru 30 da fara raya yankin Pudong na birnin Shanghai, da aiwatar da manufar bude kofa a yankin. Za mu iya ganin sakamakon nagari da za a iya samu, ta hanyar yin gyare-gyare da rungumar sabuwar manufa, ta hanyar misali da yankin Pudong.

A baya yankin Pudong karkara ce ta birnin Shanghai, inda matsayin tattalin arzikin wurin bai wuce matsayin kauyuka ba. Sai dai, bayan da aka fara amfani da manufar kebe wannan yanki don raya masana’antu da ciniki, gami da kimiyya da fasaha, yawan GDPn yankin ya haura daga Yuan biliyan 6 a shekarar 1990, zuwa Yuan biliyan 1270 a shekarar 2019. Yanzu haka yankin, da fadinsa ya kai kashi 1 bisa 8000 na fadin kasar Sin, yana samar da GDPn da ya kai kashi 1 cikin kashi 80 na GDPn daukacin kasar, da kashi 1 cikin kashi 15 na yawan kayayyakin da ake shigo da fitar da su a kasar. Ban da wannan kuma, tsawon rayukan jama’ar yankin ya karu daga shekaru 76 a shekarar 1993 zuwa shekaru 84 a yanzu. Kana fadin gidan zama da kowane mutum ke samu a yankin ya karu daga mita 15 a shekarar 1993 zuwa mita 42 a halin yanzu. Wadannan alkaluma sun nuna cewa, aiwatar da sabuwar manufar bude kofa, da raya masana’antu da ciniki, ya sa yankin Pudong ya samu ci gaba matuka, a bangarorin tattalin arziki, da zaman al’umma.

Idan mun dubi tarihi na kasar Sin, za mu ga cewa, yadda aka yanke shawarar bude kofa a yankin Pudong ba abu ne mai sauki ba. Saboda a lokacin, wato shekarar 1990, yanayin duniya yana da sarkakiya sosai. Yayin da tarayyar Sobiet USSR ke daf da rushewa, lamarin da ya haifar da tashin-tashin hankali a gabashin Turai. Kana kasashe da dama suna tsoron fuskantar hadari a fannin tattalin arziki, don haka ba su son zuba jari a sauran kasashe. A cikin wannan yanayi ne, kasar Sin ta tsai da kudurin kebe yankin Pudong don gwada wasu sabbin manufofi, da matakan gyare-gyare. A cikin wannan yanki ne, an kafa kasuwar hada-hadar kudi ta farko ta kasar Sin, da bankin kasashen waje na farko na kasar, da yankin ciniki cikin ’yanci na farko na kasar, da dai sauransu. Wadannan gwaje-gwajen da aka yi, sun shaida yadda kasar Sin take rungumar sauye-sauyen yanayi, da ci gaba da aiwatar da gyare-gyare, don daidaita matsalolin da ake fuskanta, da samun dauwamammen ci gaba a kasar. Misali na yankin Pudong na kasar Sin ya nuna cewa, duk mai nema yana tare da samu. Idan ana son kawo sauye-sauye, to, dole a rungumi sabbin manufofi, da kokarin gudanar da gyare-gyare ba tare da tsoron wahala ba.

Yadda gwamnatin tarayyar Najeriya ta rungumi yarjejeniyar AfCFTA a wannan karo, ya nuna niyyar kasar ta shiga a dama da ita a kokarin hadin kan tattalin arzikin kasashen Afirka, da yadda ake neman daidaita manufofi a fannonin ciniki da kasuwanci, don samun dauwamammen ci gaba a kasar. Muna sa ran ganin wannan sabon matakin da aka dauka zai kawo sauye-sauye da ci gaba ga yanayin tattalin arziki da zaman al’umma na kasar. (Bello Wang)

Bello