logo

HAUSA

Ta yaya yankin Pudong na birnin Shanghai zai yi kokarin taimakawa ayyukan kirkire-kirkire?

2020-11-15 17:18:07 CRI

Ta yaya yankin Pudong na birnin Shanghai zai yi kokarin taimakawa ayyukan kirkire-kirkire?

Kwanan nan, an cika shekaru 30 da rayawa gami da bude kofar yankin Pudong na birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin ga kasashen waje. A daidai wannan muhimmin lokaci, an baiwa yankin wani sabon aiki, wato ya zama babban karfi na yin kirkire-kirkire, har ya zama sabon wuri na gudanar da ayyukan kirkire-kirkiren. Ana ganin cewa, ayyukan kirkire-kirkire zasu taka muhimmiyar rawa a shirye-shiryen raya yankin Pudong a nan gaba, al’amarin da ya dace da babban burin da har kullum kasar Sin take kokarin neman cimmawa, wato raya kasa don ta zamanto kasa mai karfin kimiyya da fasaha.

An yi hasashen cewa, a nan gaba, yankin Pudong zai ci gaba da maida hankali kan sabbin fasahohin zamani a duk fadin duniya, da kara yin ayyukan kirkire-kirkire, a wani kokari na taimakawa ga samun babban ci gaba a wasu fannonin da suka shafi muhimman fasahohi. Bugu da kari, yankin Pudong zai himmatu wajen maida nasarorin nazarin kimiyya da fasaha don su zama manyan sana’o’i masu taka rawa.

Ta yaya yankin Pudong na birnin Shanghai zai yi kokarin taimakawa ayyukan kirkire-kirkire?

Yankin Pudong ya samu dimbin nasarori a shekaru 30 da suka wuce, duba da yadda yake kokarin habaka bude kofarsa ga kasashen waje, a nan gaba ma haka zai ci gaba da yi. Babu shakka ba za a takaita yin kirkire-kirkire a cikin gida kawai ba, maimakon haka, za a zurfafa yin gyare-gyare a gida da fadada bude kofa ga kasashen waje, ta yadda Pudong zai zama muhimmin bangare na bunkasa tattalin arzikin cikin gidan kasar Sin kana muhimmiyar mahada ta bunkasa tattalin arzikin cikin gida da na kasashen waje, wanda zai sa kaimi ga samar da ingantaccen ci gaban kasar. (Murtala Zhang)