logo

HAUSA

Yankin ciniki maras shinge mafi girma da aka fara ginawa wata babbar nasara ce ta fuskar aiwatar da ra’ayin kasancewar bangarori daban-daban a duniya

2020-11-15 21:34:33 CRI

Yankin ciniki maras shinge mafi girma da aka fara ginawa wata babbar nasara ce ta fuskar aiwatar da ra’ayin kasancewar bangarori daban-daban a duniya

Bayan cika shekaru 8 a yau Lahadi, wato ranar 15 ga watan Nuwambar shekara ta 2020, an rattaba hannu kan yarjejeniyar kawancen raya tattalin arzikin shiyya ko kuma RCEP a takaice. Ke nan, an kaddamar da aikin gina yankin ciniki maras shinge wanda ke kunshe da mutane mafi yawa kuma wanda ke da makoma mafi haske a duniya.

Yankin ciniki maras shinge mafi girma da aka fara ginawa wata babbar nasara ce ta fuskar aiwatar da ra’ayin kasancewar bangarori daban-daban a duniya

Ko menene wannan yankin zai kawowa duniya? Ba zurfafa dunkulewar tattalin arzikin shiyyar bai daya kawai zai yi ba, kuma ba sa kaimi ga farfadowar tattalin arzikin duniya kawai zai yi ba, har ma zai nuna babbar niyyar kasashen shiyyar, na goyon-bayan ra’ayin kasancewar bangarori daban-daban da gudanar da cinikayya marar shinge. Hakan zai nunawa duniya cewa: fadada bude kofa da inganta hadin-gwiwa hanya ce madaidaiciya da za’a bi wajen neman samun moriya tare.

Yankin ciniki maras shinge mafi girma da aka fara ginawa wata babbar nasara ce ta fuskar aiwatar da ra’ayin kasancewar bangarori daban-daban a duniya

Ganin yadda wasu ‘yan siyasar Amurka suke yunkurin nuna ra’ayin bada kariya ga harkokin kasuwanci da ra’ayin kashin kai, da kuma barkewar annobar COVID-19, tattalin arzikin duniya yana fuskantar koma-baya sosai. Bisa sabon hasashen da asusun bada lamuni na duniya wato IMF ya yi, tattalin arzikin duniya zai ragu da kaso 4.4 a shekarar da muke ciki. A irin wannan lokaci, daddale yarjejeniyar RCEP yana nufin cewa, kasuwar gabashin nahiyar Asiya mai karfin tattalin arziki kana mai kyakkyawar makoma, tana adawa da ra’ayin bada kariya ga harkokin cinikayya, al’amarin da zai taimaka ga farfadowa da kyakkyawan fata na samun bunkasuwar tattalin arzikin duniya.

Da ma an ce kyawun alkawari cikawa ne. A bangaren kasar Sin kuma, daddale yarjejeniyar RCEP ya shaida cewa, shugabannin kasar sun cika alkawarin da suka dauka na ci gaba da bude kofar kasar ga kasashen ketare. Wato kasar Sin zata ci gaba da fadada bude kofarta ga kasashen waje, da baiwa sauran kasashe damammakin more bunkasuwarta.(Murtala Zhang)