logo

HAUSA

Batun allurar rigakafin COVID-19 a Brazil na da alaka da siyasa

2020-11-14 17:22:09 CRI Hausa

Batun allurar rigakafin COVID-19 a Brazil na da alaka da siyasa

A ranar 9 ga wata, hukumar lafiya ta kasar Brazil ta sanar da dakatar da aikin gwajin allurar rigakafin cutar COVID-19 da kamfanin SINOVAC ke aiwatarwa a kasar kwatsam, bisa dalilin rasuwar wani ma’aikacin sa kai dake cikin aikin. Matakin da ya jawo hankalin bangarori daban-daban tare da baza jita-jita da dama, har wasu ’yan siyasar kasar na ganin cewa, lamarin na da alaka da ingancin allurar kasar Sin. Amma, bayan ’yan sanda sun yi bincike, sun bayyana cewa, mutumin ya mutu sanadiyyar kisan kai da kai. Ban da wannan kuma, kungiyar nazari ta Butanta ta kasar ta gabatar da rahoton cewa, babu matsala dangane da ingancin allurar, kuma ba ta da alaka da mutuwar wannan mutumin.

Wasu kafofin yada labarai na kasar Brazil na bayyana cewa, wannan batu na da alaka da burin siyasa. Kwayar cutar ba ta da ra’ayin siyasa. Siyasantar da batun allurar zai lahanta moriyar al’umma. Masana a kasar Brazil na da wayewar kai game da wannan batu. Da fashin baki na kafar yada labarai na Rede Globo Cruise ya nuna cewa, dakatar da aikin gwajin allurar da Sin ta samar ba tare da wani dalili ba, ya yi kama da toyar mai a mance da albasa. Darektan kungiyar rigakafin cututuka ta kasar Renato Kfouri ya bayyana cewa, kimiyya ba ta da ra’ayi a siyasance, yana mai cewa, bai kamata a nuna bambancin ra’ayi kan allurar bisa asalinta ba.

A halin yanzu, cutar COVID-19 na ci gaba da dabaibaye fadin duniya, inda miliyoyin jama’a ke matukar bukatar allurar rigakafi.

A matsayin kasar dake sahun gaba a duniya a wannan fanni, Sin tana gudanar da aikin gwajin nau’o’in alluranta 4 a duniya, wadanda suka bayyana ingancinsu a matakin 3, abin da ya samu karbuwa daga al’ummar duniya. A watan Satumba, kasar hadaddiyar daular Larabawa ta sanar da yin amfani da allurar kasar Sin cikin gaggawa, rahoton da ta gabatar na nuna cewa, gwamnatin ta amince da ingancin allurar kasar Sin. (Amina Xu)