logo

HAUSA

Hadin gwiwa tsakanin Sin da Kasashen Afirka ta samu sakamakon a zo a gani karkashin inunwar FOCAC

2020-11-14 19:46:12 CRI

Hadin gwiwa tsakanin Sin da Kasashen Afirka ta samu sakamakon a zo a  gani karkashin inunwar FOCAC

Bana ake cika shekaru 20 da kafuwar dandalin tattauna hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka, FOCAC. A yayin wani taron manema labaru da aka shirya a jiya Juma’a 13 ga wata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana cewa, karkashin inuwar FOCAC, hadin gwiwar da aka yi tsakanin kasashen Sin da Afirka ta samu sakamakon a zo a gani wajen gina wata al’ummar bil Adam dake da makoma mai haske a fannonin kiwon lafiya, da neman bunkasuwa da kuma shawo kan matsalolin da suke fuskanta tare, wadanda suka samar da moriya ga al’ummunsu kwarai. Kamar yadda Mr. Wang Wenbin ya fadi, a cikin shekaru 20 da suka gabata, huldar dake tsakanin kasashen Sin da Afirka ta samu ci gaba, har ma ta kasance kamar “a kan samu dimbin ’ya’ya daga itacen dake da saiwa mai karfi matuka.”

A yayin taron, Mr. Wang Wenbin ya kara da cewa, “idan an kwatanta shekaru 20 da suka gabata, jimillar darajar cinikayya tsakanin Sin da Afirka ta kai dalar Amurka biliyan 208.7, wato ya karu da ninki 20. Sannan yawan jarin da bangaren Sin ya zuba a Afirka kai tsaye ya kai dalar Amurka biliyan 49.1, wato ya karu da ninki 100. Bugu da kari, tsawon layin dogo da na hanyoyin mota da kamfanonin kasar Sin suka shimfida a kasashen Afirka, dukkansu sun wuce kilomita 6000, a yayin da suka gina tasoshin ruwa kusan 20, da manyan ayyukan samar da wutar lantarki fiye da 80. Dadin dadawa, a cikin wadannan shekaru 20 da suka gabata, yawan daliban kasashen Afirka da suka samu kudin alawus daga gwamnatin kasar Sin suka kuma yi karatu a kasar Sin ya kai wajen dubu 120. A waje daya, yawan ma’aikatan jinya da kasar Sin ta tura wa kasashen Afirka 48 ya kai kimanin dubu 21, wadanda suka ceci marasa lafiya wajen miliyan 220 a nahiyar.”

Wadannan alkaluma sun bayyana cewa, ba cin gajiyar hadin gwiwar dake tsakaninta da kasashen Afirka kadai kasar Sin ke yi ba, har ma da ingiza kasashen Afirka su kara yin hadin gwiwa tsakaninsu domin neman samun bunkasuwa tare.

Hadin gwiwa tsakanin Sin da Kasashen Afirka ta samu sakamakon a zo a  gani karkashin inunwar FOCAC

Bugu da kari, karkashin inuwar FOCAC, kasashen Sin da Afirka na kara hadin gwiwa a dandalin diflomasiyya da na siyasa na kasa da kasa, inda su kan dauki matsaya daya domin tsaron moriyar yawancin kasashe masu tasowa. Alal misali, a yayin wani taron muhawara na kwamiti na uku na babban taron MDD da aka yi a ran 5 ga watan Oktoban bana, wakilin kasar Sin dake MDD, jakada Zhang Jun ya wakilci kasashe masu tasowa 26, ciki har da wasu kasashen Afirka kamar Angola, da Burundi, da Eritrea da Namibia da Sudan ta kudu, da Sudan da Zimbabwe, inda ya gabatar da wani jawabi, da ya zargi wasu kasashen yammacin duniya, kamar kasar Amurka da keta hakkin bil Adama.

A lokacin da kasar Sin take matsanancin hali na dakile annobar COVID-19 a bana, kasashen Afirka, masu girma, ko kanana, mafiya karfi ko rauni, dukkansu sun yi kokarin tallafawa kasar Sin. Sabo da haka, a lokacin da kasashen Afirka suke cikin mawuyacin hali na dakile annobar, daga farko dai, tawagogin jinya na kasar Sin wadanda suke kasashen Afirka 45 sun shirya wa masu aikin jinya na kasashen Afirka kwas-kwas na koyon ilmin dakile annobar har sau 400. Gwamnati da kamfanoni da wasu asusu na kasar Sin ma sun samar da dimbin kayayyakin tunkarar annobar, tare da tura tawagogin kwararru zuwa kasashen Afirka sau da dama. Sakamakon haka, Mr. Tedros Adhanom Ghebreyesus, babban direktan kungiyar kiwon lafiya ta kasa da kasa WHO ya yabawa kasar Sin tare da gode mata, inda ya ce bayan barkewar annobar, a kullum kasar Sin na tsayawa da Afirka, ba ma kawai ta tura kwararru, da samar da bayanai da magungunan gwada annobar ba, har ma ta dauki matakan soke wasu basusukan da wasu kasashen Afirka suka ci domin tallafa musu wajen farfado da tattalin arzikinsu.

A cikin sakon da suka mika wa juna a ran 12 ga watan Oktoban bana, shugaba Xi Jinping na kasar Sin da takwaransa na kasar Senegal Macky Sall, kuma shugaban karba-karba na sashen Afirka na dandalin FOCAC sun nuna cewa, a cikin shekaru 20 da suka gabata, dandalin FOCAC ya kasance tamkar wata muhimmiyar tutar dake alamta yadda ake hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. Muna cike da imanin cewa, a cikin shekaru 20 masu zuwa, dandalin zai ci gaba da taka rawarsa ta gani wajen kara bunkasa huldar dake tsakanin Sin da Afirka, da kuma moriyar al’ummunsu. (Sanusi Chen)