logo

HAUSA

Sharhi: Wani nazari kan ingantaccen tsarin yankin Pudong na bude kofarsa

2020-11-13 14:47:48 CRI

“Ya kamata a kara zage damtse wajen ganin yankin Pudong ya kasance zakaran gwajin dafi kan manufar yin gyare-gyare da kara bude kofa ga kasashen ketare” “Haka kuma, ya kamata yankin Pudong, ya yi kokarin zama abin misali, dake nuna imanin turbar da Sinawa ke bi, da tsari, da ka’ida da al’adar gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin”.  A jawabin da ya gabatar yayin bikin cika shekaru 30 da raya da bude kofar yankin Pudong dake birnin Shanghai da aka gudanar a jiya Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana fatansa na ganin yankin ya kara bunkasa. 

 

Sharhi: Wani nazari kan ingantaccen tsarin yankin Pudong na bude kofarsa

In an waiwayi shekaru 30 da suka wuce, za a yi mamakin ganin cewa, yankin ya janyo jarin waje da ya kai dalar Amurka biliyan 102.95, tare da kamfanoni masu jarin waje dubu 36.2 daga kasashe da shiyyoyi 170, a yayin da wasu kamfanonin kasa da kasa 350 suka kafa hedkwatocinsu na shiyya a birnin. Baya ga haka, 346 daga cikin fitattun kamfanonin duniya 500 suna da ayyukan da suka zuba jari a birnin. Kamar yadda shugaba Xi Jinping ya bayyana ne, nasarorin da aka cimma cikin shekaru 30 da suka gabata bayan da aka raya da kuma bude kofar yankin Pudong, sun shaida ingancin tsarin gurguzu mai sigar musamman ta kasar Sin.

Tun farkon fari, an raya yankin Pudong ne da manufar “bunkasa cudanyar tattalin arziki da kasashen duniya”, manufar da ta kawo nasarorin ga yankin Pudong.

Bisa ga shirin da kasar Sin ta tsara, ya zuwa tsakiyar karnin da muke ciki, za a raya kasar Sin ta yadda za ta zama kasa mai karfi da ke bin tsarin gurguzu daga dukkan fannoni. To, a yayin da ake fuskantar manyan sauye-sauye a duniya, da kuma yadda kasar Sin ke gaggauta gina sabon tsarin ci gabanta, shin yaya yankin Pudong zai kara cin moriyar juna tare da kasashen duniya a nan gaba?  Babu shakka,  “ingantaccen tsarin bude kofa” ya zama abin da ya kamata a mai da hankali a kai.

Sharhi: Wani nazari kan ingantaccen tsarin yankin Pudong na bude kofarsa

Tun bayan babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin a karo na 18, an kafa yankin gwajin ciniki marar shinge tare kuma da gabatar da takardar jerin fannonin da aka haramtawa baki ‘yan kasuwa su zuba jari, takardar da ta kasance ta farko da kasar Sin ta gabatar, kafin daga bisani an yi ta yayata fasahohin da yankin na Pudong ya samu wajen yin gwajin bude kofarta bisa tsari mai inganci”. A gun bikin murnar da aka gudanar a jiya, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, “ kamata ya yi yankin Pudong ya inganta bude kofarsa, tare da kara samun karfin hadin gwiwa da takara a duniya”, furucin da ya takaita nasarorin da yankin Pudong ya samu cikin shekaru 30 da suka wuce, wanda kuma ya nuna hanyar da ya kamata yankin ya bi a nan gaba.

Makomar yankin Pudong ita ce zama muhimmin bangare na bunkasa tattalin arzikin cikin gidan kasar Sin kana muhimmiyar mahada ta bunkasa tattalin arzikin cikin gida da na kasashen waje.

To, sai dai “muhimmin bangare” da kuma “muhimmiyar mahada” na nufin za a kyautata kwarewarsa wajen raba jari da bayanai da fasahohi da kwararru da kuma kayayyaki. A game da wannan, yankin Pudong yana da cikakken imani. Sanin kowa ne cewa, a yankin akwai cibiyar hada-hadar kudi ta Lujiazui da kuma cibiyar nazarin kimiyya ta Zhangjiang wadanda suke da kwarewa wajen raba kayayyaki da kirkire-kirkiren fasahohi zuwa sassan duniya. Baya ga haka, kamfanonin kasa da kasa 350 da suka kafa hedkwatocinsu na shiyya a yankin Pudong za su gano sabon madogarar ci gabansu a yayin da kasar Sin ke kokarin bunkasa tattalin arzikin cikin gida tare da hade kasuwar cikin gida da ta ketare.

Ma iya cewa, nan da shekaru 30 masu zuwa, kasashen duniya za su iya ganin yadda yankin na Pudong da ma kasar Sin baki daya za su samu karin kuzari da bunkasa, tare kuma da gano karin damammaki na samun ci gaban kansu.(Lubabatu)