logo

HAUSA

Sharhi: Kasar Sin da ta bude kasuwarta

2020-11-13 20:19:47 CRI

“Kofi na Ruwanda, gilashi na kasar Czech, sai kuma madarar rakuma daga Dubai…Wadannan kayayyakin da ba a yawan samunsu a kasuwar kasar Sin, yanzu suna shiga hannun masu sayayya na kasar Sin ta yanar gizo cikin sauki.” Mr. Huang Lei, manazarci na kamfanin Tmall.com (daya daga cikin kamfanonin sayar da kaya ta yanar gizo mafi girma na kasar Sin) ne ya yi wannan bayani a yayin da yake tsokaci a kan bikin sayayya mafi girma na kasar Sin ta wannan shekara.

Sharhi: Kasar Sin da ta bude kasuwarta

Ranar sayayya ta kasar Sin, wadda ta yi kama da ranar "Black Friday" da ke gudana a yammacin duniya, rana ce da masu sayar da hajoji ke samar da garabasa ga masu sayayya, wadda kuma ta kan fado a ranar 11 ga watan Nuwamban kowace shekara. Sai dai a wannan shekara, an tsawaita lokacin bikin na sayayya, wato an fara ne daga ranar 1 ga wata, don ba masu sayayya isasshen lokaci wajen zabar kayan da suke bukata.

Sai dai abin lura shi ne a wannan shekara, yawan kayayyakin kirar kasashen ketare da aka sayar a yayin bikin ya karu matuka, inda kamfanoni dubu 25 na ketare sun hada gwiwa da kamfanin Tmall.com wajen tallata kayayyakinsu. Alkaluma na nuna cewa, daga ranar 1 zuwa 11 ga wata na tsakar ranar, yawan kayayyakin da aka sayar ta kafar Tmall.com wadanda aka shigo da su kasar Sin daga kasashen waje, sun karu da kaso 47.3%, kuma kudin ciniki na kayayyakin wasu tambura 180 da aka shigo da su daga ketare ya zarce miliyan 10 kowanensu. Alkaluman da kamfanin JD.com, wani babban kamfanin sayar da kayayyaki ta yanar gizo na kasar Sin ya samar sun kuma nuna cewa, a yayin bikin sayayya na bana, kamfanin ya sayar da nau’o’in kayayyaki sama da dubu 500 da aka shigo da su daga kasashe da shiyyoyi sama da 100.

Idan ba a manta ba, a ranar 10 ga wata ne, aka rufe bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin (CIIE) a karo na uku, bikin da ya baje kolin kayayyaki iri iri da ake shigo da su kasar Sin, ciki har da nau’o’in kayayyaki daga kasashen Afirka, kamar kofi na Habasha da zumar Zambia da dai sauransu. Haka kuma a yayin bikin, kamfanin Gera mai sai da kofi na kasar Habasha ya daddale yarjejeniya tare da kamfanin Tmall.com, wato ke nan ya samu damar sayar da kayan da ya nuna a wajen bikin ta kafar kamfanin Tmall.com.

Sharhi: Kasar Sin da ta bude kasuwarta

 

Don neman yin amfani da damar bikin sayayya na wannan shekara, ma’aikatan kamfanin Gera sun gaggauta tura kayansu daga gida Afirka, kuma hakarsu ta cimma ruwa, daga karshe sun yi nasarar sayar da kayansu a yayin bikin sayayya na wannan shekara.

Kevin Zhu, jami’in da ke kula da bangaren sai da kaya ta yanar gizo na kamfanin ya bayyana cewa, a baya a kan biya kudi mai yawa wajen fitar da waken kofi zuwa ketare, amma a wannan karo, ta kafar kamfanin Tmall.com, kudin da aka biya ya ragu sosai, matakin da kuma ya kara kudin shigar manoman wurin.

Alkaluman da Tmall.com ya fitar sun yi nuni da cewa, daga ranar 1 zuwa 11 ga wata, kudin cinikin da aka yi ta kamfanin ya kai yuan biliyan 498.2 (kwatankwacin dala biliyan 75.27), wanda kusan ya ninka na bara har sau biyu. Sai kuma alkaluman da kamfanin JD.com ya fitar sun shaida cewa, kudin da aka biya na odar kayayyaki daga wajensa a yayin bikin sayayya na wannan shekara ya zarce yuan biliyan 271.5. Lamarin da ya shaida karin farfadowar tattalin arzikin kasar Sin da ma babbar kasuwarta ga kasashen duniya.

Sharhi: Kasar Sin da ta bude kasuwarta

A yayin bude bikin CIIE na wannan shekara, shugaban kasar Afirka ta kudu Ciril Ramaphosa ya gabatar da jawabi ta yanar gizo, inda ya ce, kasashen duniya na kara bukatar damar da za ta taimaka wajen zuba jari da ciniki a sakamakon annobar Covid-19 a wannan shekara. Duk da cewa ana fuskantar annobar a sassan duniya, amma kasar Sin ta gudanar da bikin CIIE a karo na uku kamar yadda aka tsara, har ma kamfanonin da suka hallarci bikin sun fi na shekarun baya, lamarin da ya shaida alkawarin da kasar Sin ta dauka na kiyaye dunkulewar tattalin arzikin duniya.

Kasar Sin ta sha nanata kudurinta na kara bude kofarta ga kasashen ketare. A daidai lokacin da ake fuskantar tabarbarewar tattalin arzikin duniya a sanadin annobar Covid-19, kasar Sin na kokarin cika alkawarinta ta yadda kasashen duniya, musamman ma kasashen Afirka da ma sauran kasashe masu tasowa za su amfana da kasuwarta, don tabbatar da ganin tattalin arzikin duniya ya farfado. (Lubabatu)