logo

HAUSA

Sin ce ke rike da matsayin mai bunkasa wasannin yanar gizo yayin da ake tsaka da yaki da annobar COVID-19

2020-11-12 10:27:40 CRI

A kwanakin baya, gaban ‘yan kallo sama da 6,000, a kuma sabon filin wasan kwallon kafa da aka kammala ginawa na “Shanghai Pudong”, wanda ya karbi ‘yan kallo a karon farko yayin wata babbar gasa, tawagar wasan yanar gizo ta koriya ta kudu ko DWG a takaice, ta samu nasara kan takwarar ta ta kasar Sin ko SN da ci 3 da 1, lamarin da ya baiwa tawagar koriya ta kudun nasarar lashe kofin duniya na shekarar 2020, na zakarun masu buga gasa ta yanar gizo ko LOL a takaice.

Sin ce ke rike da matsayin mai bunkasa wasannin yanar gizo yayin da ake tsaka da yaki da annobar COVID-19

Nasarar DWG ta kasance ta 6 ga kasar koriya ta kudu, a wannan gasa da masu sha’awar wasannin yanar gizo suka fi kallo, tun kaddamar da  wasannin ta yanar gizo a shekarar 2011, wanda hakan ya dakatar da burin Sin na shigewa gaba a gasar karo na 3 a jere, bayan da kasar ta yi nasarar lashe gasannin “Invictus Gaming” ko IG, da kuma “FunPlus Phoenix” ko FPX a takaice a shekaru 2 da suka gabata.

To sai dai kuma duk da hakan, rashin nasarar da Sin ta gamu da ita a wannan fage, ba ta hana kasar zama wadda ke kan gaba ba, a fannin samun saurin bunkasar wasannin yanar gizo ko “eSports” a takaice, musamman ma a lokacin da ake shan fama da cutar numfashi ta COVID-19 a wannan shekara ta bana. Rahotanni da dama a fannin na cewa, a bana Sin ta sha gaban arewacin Amurka a fannin raya kasuwannin wasannin yanar gizo ko “eSports” musamman bangaren masu kallo da tara kudaden shiga a fannin.

A cewar Newzoo, daya daga manyan masu nazari a fannin wasannin yanar gizo a duniya, ya bayyyana cewa, adadin kudaden shiga a fannin wasannin yanar gizo a duniya zai karu zuwa dalar Amurka biliyan 1.1 a shekarar nan ta 2020, karuwar da ta kai ta kaso 15.7%, daga dala miliyan 950.6 da sashen ya samu a shekarar 2019, kuma Sin ce ke kan gaba a fannin samar da kudaden shigar bangaren, inda ta samar da jimillar dalar Amurka dala miliyan 385.1 a shekarar ta 2020.

Baya ga kasar Sin, yankin arewacin Am

urka ne ke biye da dalar Amurka miliyan 252.8, sai kuma yammacin turai mai adadin kudade da suka kai dala miliyan 201.2.

Yayin gasar LOL da aka kammala ba da jimawa ba, an ga yadda wasannin yanar gizo ke kara samun karbuwa sosai tsakanin al’ummar kasar Sin.

Sakamakon yanayin harkar kiwon lafiya da ake ciki a yanzu, wasan karshe da ya gudana a ranar 31 ga watan Oktoba ne ya samu shigar ‘yan kallo, kuma ko shi ma mutane 6,312 kacal aka baiwa damar shiga filin wasa na Pudong domin kallon wasan na karshe.

Sama da mutane miliyan daya ne suka tura bukatar su ta shiga kallon wasan da ya gabata cikin sa’oi 4 da bude damar hakan, kana mutane miliyan 3.2 suka shiga cacar da aka buga game da wasan.

Wata matashi mai suna Fang Yan, ‘yar shekaru 20 da haihuwa dake karatu a kwaleji, kuma take zaune a garin Ma'anshan na lardin Anhui ta bayyana cewa "Ina cikin aji lokacin da na samu sakon cewa ina cikin wadanda suka samu gurbin kallon wasan na karshe. A gaskiya da na dauka yaudara ce. Ban yi tsammanin samun irin wannan sa’a ba".

Shi ma Zhou Zhe'an, matashi dan makaranta mai shekaru 18 da haihuwa, yana cikin mazauna birnin Shanghai su 6,000 da suka samu halartar wasan na karshe da ya gudana a filin wasa na Pudong, ya kuma yi sa’a domin mahaifin sa ma ya samu irin wannan dama.

Mahaifin sa ya ce, "Na zabi zuwa nan tare da da na, saboda ina son sanin mene ne matasa ke sha’awa. Hanya ce ta cudanya da juna da fafada fahimtar juna,".

Lokacin da aka fara wasan na karshe da yammacin ranar Asabar din karshen makon jiya, an kalla, tare da tattaunawa kan sa ta yanar gizo, tsakanin miliyoyin ‘yan kallo.

Sin ce ke rike da matsayin mai bunkasa wasannin yanar gizo yayin da ake tsaka da yaki da annobar COVID-19

Alkaluman kididdiga na Bilibili, dandalin yanar gizo dake yada bayanai game da wasan, mai kuma ikon mallakar yada shi kan kwangilar shekaru 3, ta kudi har rmb miliyan 8, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 1.2, ya nuna cewa, a lokaci guda, akwai masu kallo daidaiku sama da miliyan 50 da suka kalli wasan tare ta yanar gizo.

A cewar Jin "Bobby" Yibo, daya daga manyan jami’an kamfanin TJ Sport, wanda ke kula da gasar “eSport” da ake gudanarwa karkashin gasannin LOL na Sin "A ganin mu, mun kammala abu dake da matukar wahalar yi. Musamman a wannan lokaci na fama da wannan annoba, Mun gudanar da gasa mai inganci kuma muna alfahari da hakan,".

A wannan shekara da annobar COVID-19 ta sanya aka dage lokacin gudanar da wasu gasanni, aka kuma soke wasu, gudanar da gasar LOL ta shekarar 2020 ta yanar gizo abun a yaba ne. Kuma ko shakka ba bu nasarar da Sin ta samu ta shawo kan annobar COVID0-19 ce ta haifar da wannan kyakkyawan sakamako.

Da yake tsokaci game da batun gasar, shi ma Nicolo Laurent dan kasar Faransa, kuma shugaban kamfanin kirkirar wasanni ta yanar gizo na “Riot Games” cewa ya yi, “Mutane da dama na gani mun baiwa wannan harka muhimmanci da yawa, amma a gani na ba wani wuri a duniya da za mu iya gudanar da wannan gasa cikin nasara sama da nan kasar Sin."

A cewar Laurent a bana, birnin Shanghai ya nuna karfin sa na zama kan gaba a duniya, a fannin wasannin yanar gizo.

An fara gudanar da gasar LOL ta duniya a nan kasar Sin a shekarar 2017, a lokacin an buga wasan karshe ne a filin wasa na kasa mai suffar shekar tsuntsu dake nan birnin Beijing, matakin da ya zamo abun misali a fannin karbuwar wasannin na yanar gizo.

Cikin shakau 3 da suka gabata, wasanni ta yanar gizo na kara samun karbuwa a kasar Sin. ‘Yan wasan kasar ma na kara nuna kwarewa, an kuma samar da manufofi daban daban na inganta gudanar da wasannin. Bugu da kari kuma, ana ta sauya tsofaffin ka’idodjin gudanar da wasan.

A watan Fabarairun wannan shekara, a hukumance Sin ta fitar da dokokin gudanar da wasannin ajin kwararru ta yanar gizo, dokokin da suka shafi mukaman “masu shiga wasan”, da kuma “masu gudanar da su”, matakin da ake kallo a matsayin muhimmin gaske ga ci gaban fannin

A shekara mai zuwa ma, za a gudanar da gasar LOL ta duniya ne a nan kasar Sin. Ko ma dai wa ye zai lashe gasar, Sin za ta ci gaba da rike kambin ta na wadda ke taka rawar gani ga bunkasuwar wasannin da ake bugawa ta yanar gizo.