logo

HAUSA

Hira da jakadan Najeriya Mai girma Baba Ahmad Jidda dangane da allurar rigakafin annobar COVID-19

2020-11-11 09:14:09 CRI

Hira da jakadan Najeriya Mai girma Baba Ahmad Jidda dangane da allurar rigakafin annobar COVID-19

An bayyana ziyarar jami'an a matsayin wata dama ta zurfafa hadin gwiwa a fannin yaki da cutar COVID-19, tare da gina managarcin tsarin kiwon lafiya tsakanin al'ummun Sin da na nahiyar Afirka.Jakadun kasashen nahiyar Afirka da ke aiki a kasar Sin da wakilan wasu cibiyoyin Afirka a kasar Sin 51, sun ziyarci babbar cibiyar gwaje gwaje da binciken rigakafin cututtuka ta kamfanin Sinopharm CNGB na Sin.

Hira da jakadan Najeriya Mai girma Baba Ahmad Jidda dangane da allurar rigakafin annobar COVID-19

Kaza lika jami'an jakadancin sun ganewa idanun su, kayan bincike da aka baje a cibiyar, da ma dajin gwaji na zamani, kana sun samu karin haske game da matakan baya bayan nan na gwajin rigakafin cutar COVID-19 da cibiyar kamfanin ke gudanarwa.

Wannan ne dai karo na farko da sakatariyar kwamitin bibiya game da ayyukan dandalin FOCAC, ya shirya wani aiki a zahiri, tun bayan barkewar cutar COVID-19.

Hira da jakadan Najeriya Mai girma Baba Ahmad Jidda dangane da allurar rigakafin annobar COVID-19

Cibiyar Sinopharm CNGB ce irin ta mafi girma a kasar Sin, kuma ta 5 a duniya baki daya, a fannin gwaje gwaje da bincike da samar da rigakafi. Wakiliyarmu Kande ta samu damar yin hira da jakadan Najeriya Mai girma Baba Ahmad Jidda dangane da ziyararsa a cibiyar da dai sauransu. (Saminu)

Tasallah Yuan