An sake komawa zaman taron hukumar WHO
2020-11-10 14:29:44 CRI
A jiya 9 ga wata ne aka sake komawa zama na 73, na hukumar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta kafar intanet, a birnin Geneva na kasar Switzerland. A jawabin da ya gabatar a gun bikin bude zaman, babban darektan hukumar, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa, gano bakin zaren warware matsalar COVID-19 a kimiyyance, tare kuma da hadin gwiwa da juna, shi ne hanya daya tilo da za a iya bi wajen shawo kan annobar a fadin duniya. Ban da haka, taron da aka yi a wannan rana, ya kuma ki amincewa da saka shawarar da wasu kasashe kalilan suka gabatar, ta "gayyatar yankin Taiwan ya halarci taron hukumar a matsayin mai sa ido cikin abubuwan da za a tattauna a gun taron". Daga ranar 9 zuwa 14 ga watan nan ne za a sake komawa zama na 73 na hukumar kiwon lafiya ta duniya(WHO). A kan gudanar da taron hukumar na tsawon makon guda a watan Mayun kowace shekara, sai dai a wannan shekara, a sakamakon annobar Covid-19, an shafe kwanaki biyu kacal ana taron a watan Mayu, inda aka mai da hankali a kan tattauna ta yaya za a shawo kan annobar. A zaman taron na wannan karo, za a kuma tattauna sauran muhimman batutuwan da suka shafi harkokin kiwon lafiya a duniya, da kuma harkokin kudi, da gyare gyare na hukumar, baya ga annobar. A jawabin da ya gabatar a gun bikin bude taron, babban darektan hukumar WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa, sama da mutane miliyan 1.2 suka halaka a fadin duniya a sakamakon annobar Covid-19. Sai dai tasirin da annobar ta haifar ga kasashe daban daban ya bambanta, a sakamakon mabanbamtan matakan da suka dauka. Ya jaddada cewa, gano bakin zaren warware matsalar a kimiyyance, tare kuma da hadin gwiwa da juna, shi ne hanya daya tilo da za a iya bi wajen shawo kan annobar Covid-19 a fadin duniya. Ya ce,"Watakila mun gaji da fama da cutar, amma cutar ba za ta gaji ba. Cutar na barna ga mutane da ba su da karfin jiki, tana kuma amfani da sauran matsalolin da muke fuskanta, da suka hada da rashin daidaito, da sabanin ra'ayi, da kuma yadda muke yin biris da ita don yakarmu. Mun gaza shawarwari da cutar, kuma ba za mu iya rufe idanunmu kawai don fatan ganin bayan ta. Hanya daya tilo da za mu iya bi ita ce mu gano bakin zaren warware matsalar a kimiyyance, tare kuma da hadin gwiwa da juna." Ban da haka, a gun zaman da aka gudanar a ranar 9 ga wata, an kuma zartas da kudurin kin saka shawarar da wasu kasashe kalilan suka gabatar ta "gayyatar yankin Taiwan ya halarci taron hukumar a matsayin mai sa ido" cikin abubuwan da za a tattauna a gun taron.
A game da wannan, kakakin zaunanniyar tawagar kasar Sin a Geneva, Mr. Liu Yuyin ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin na daukar dukkan matakan da suka wajaba, wajen kiyaye lafiyar al'ummarta a yankin Taiwan. "Bayan barkewar annobar, mun fara ne da gayyato masanan ilmin kiwon lafiya na yankin Taiwan da su kai ziyara birnin Wuhan na lardin Hubei, kuma kawo yanzu, an sanar da yankin Taiwan kan yanayin annobar har sau 245. Ya ce, "Mahukuntan yankin Taiwan na yunkurin halartar taron, tare da habaka kujerunsa a duniya ne bisa abin da suka furta, na wai akwai 'gibin rigakafin cutar'. Sai dai yadda taron hukumar WHO ya ki amincewa da shawarar da wasu kasashe kalilan suka gabatar a shekaru da dama a jere, ya bayyana yadda kasa da kasa suka cimma daidaito, game da kiyaye ka'idar kasar Sin daya tak a duniya."