logo

HAUSA

Kimiyya da fasaha na da gagarumin tasiri wajen inganta rayuwar jama'a ta hanyoyi da dama

2020-11-10 19:39:53 CRI

Kimiyya da fasaha na da gagarumin tasiri wajen inganta rayuwar jama'a ta hanyoyi da dama

10 ga watan Nuwamban kowacce shekara, rana ce da hukumar bunkasa ilimi da kimiyya da raya al'adu ta MDD ta ware a matsayin ta Kimmiya domin samun ci gaba da zaman lafiya. An ware wannan rana ce da zummar bayyana irin muhimmiyar rawar da kimiyya ke takawa a cikin al'umma da kuma bukatar kara muhawara kan batutuwan da suka shafi kimiyya. Haka zalika, tana bayyana irin muhimmanci da tasirin kimiyya ke yi a cikin rayuwar yau da kullum.

A yunkurin hada kimiyya da al'umma, ranar na kokarin tabbatar da jama'a na sane da irin ci gaban da aka samu a fannin kimiyya da kuma bayyana rawar da masana kimiyya ke takawa wajen kara fahimtar da mutane game da duniya da hanyoyin masu dorewa na kiyaye al'umma. Ranar a bana, ta zo a lokacin da aka ga irin rawar da kimiyya da fasaha suka taka wajen yaki da annobar COVID-19 da ta barke a farkon shekarar nan. Sai dai kuma, akwai bukatar kara inganta yadda duniya ke amfani da kimiyya da fasaha wajen warware kalubalen dake tunkarar duniya, kamar COVID-19. Haka zalika, akwai bukatar kara samun fahimta da hadin gwiwa tsakanin masana kimiyya da gwamnatoci da ma al'umma. Aminci daga al'umma na da matukar muhimmanci ga nasarar kimiyya da fasaha. Idan har aka samu amincewar jama'a da kuma kaucewa yada jita-jita, bayanan masana kimiyya za su yi matukar tasiri wajen kyautata zaman rayuwa da muhalli. Da a ce akwai aminci da kuma yarda da bayanan kimiyya da fasaha, da cutar COVID-19 ba ta yi mummunan tasirin da ta yi a yanzu ba.

Kimiyya da fasaha na da gagarumin tasiri wajen inganta rayuwar jama'a ta hanyoyi da dama

A don haka ne wannan rana ke mayar da hankali sosai wajen inganta hadin gwiwa a ciki da wajen kasashe wajen musayar ilimin kimiyya da fasaha da sabunta kudurin gwamnatoci na amfani da kimiyya domin amfanin al'umma da kuma jan hankali game da kalubalen da bangaren ke fuskanta.

Ajandar maradun ci gaba masu dorewa da ake son cimmawa zuwa 2035 na da nufin samar da kyakkyawar makoma ga daukacin al'umma. Wanda ya yi da ajandar kasar Sin ta gina al'umma mai makoma ta bai daya ga dukkan bil adama, wanda ake ganin na bukatar sabbin dabarun da manufofi da suka dogara da kimiyya da fasaha. A kuma wannan lokaci da ake kira da kara ba kimiyya da fasaha damar taka rawa yadda ya kamata ne, gwamnatin kasar Sin cikin shirin raya tattalin arziki da rayuwar al'ummar Sinawa na shekaru biyar karo na 14, ta ce ya zama wajibi ta dogara da kanta a fannin kimiya da fasaha, ta yadda za ta kara kyautata rayuwar jama'a da tunkarar manyan kalubalen dake gaban duniya. (Faeza Mustapha)