Aliyu Haidar: Ina so in yi koyi daga mutanen Sin!
2020-11-10 14:24:04 CRI
A cikin shirinmu na wannan mako, Murtala Zhang ya zanta da Aliyu Haidar, wani dalibi dan asalin karamar hukumar Dala dake jihar Kanon tarayyar Najeriya, wanda a yanzu haka yake karatun digiri a jami'ar nazarin kimiyya da fasaha ta Jiangxi wato Jiangxi University of technology a turance a birnin Nanchang.
A zantawar tasu, Aliyu Haidar ya bayyana dalilin da ya sa ya zabi kasar Sin don ci gaba da karatu, sa'annan ya ce, abun da ya fi burge shi a nan kasar, shi ne ganin yadda Sinawa ke maida hankalinsu kan aiki, wato kowa ya yarda da aikinsa, tare da ba shi muhimmanci ba tare da wasa ko bata lokaci game da duk wani abun da ya shafi aiki ba, a cewarsa wannan shi ne daya daga cikin dalilan da suka sa kasar Sin ta samu babban ci gaba.
Har ila yau, ya yi kira ga al'ummar Najeriya dake ciki da wajen kasar, da su yi koyi da wannan kyakkyawar dabi'a ta Sinawa.(Murtala Zhang)