logo

HAUSA

Sayar Da Kaya Ta Hanyar Watsa Bidiyo Kai Tsaye Ya Shaida Ci Gaban Kasuwannin Sin

2020-11-08 19:56:03 CRI

 

Sayar Da Kaya Ta Hanyar Watsa Bidiyo Kai Tsaye Ya Shaida Ci Gaban Kasuwannin Sin

"Cikin minti 3 an sayar da kayayyakin da darajarsu ta kai Yuan miliyan 3.5. Da farko dai na zaci jimillar ba ta yi daidai ba. Saboda Yuan miliyan 3.5 ya kusan kai darajar dukkan kayayyakin da muka sayar cikin shekara guda a baya! " Ko da yake ya riga ya fita daga dakin watsa bidiyo na kai tsaye, amma Zheng Junjie, darekta mai kula da kasuwannin kasar Sin na wani babban kamfanin samar da giya na kasar Sifaniya, yana ci gaba da kasancewa cikin tsima. Yayin da ake gudanar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su cikin kasuwannin kasar Sin karo na 3 a birnin Shanghai na kasar Sin, ya halarci wani shirin bidiyon na tallata kayayyakin kasashe daban daban da babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin CMG ya tsara. Abin da ya ba shi mamaki shi ne, yayin shirin bidiyon da aka watsa kai tsaye a daren jiya, an sayar da giyar da yawansu ya kai kwalaba dubu 200.

Ta wannan shirin bidiyo na tallata kaya, mutanen duniya sun shaida wani cikakken karfin da Sinawa suke da shi a fannin sayen kaya. Saboda a cikin irin makamancin shirin guda biyu da kamfanin CMG ya gabatar, a gefen bikin CIIE, an samu sayar da kayayyakin da darajarsu ta kai Yuan miliyan 140, inda jama'ar kasar Sin sun sayi kayayyaki masu inganci na kasashen Italiya, da Rasha, da Jamus, da Faransa, da dai sauransu, ta kafar shafin yanar gizo ta Intanet. Yanzu haka ana watsa shirin bidiyo na tallata kayayyaki sosai a bikin CIIE karo na 3. Ta wannan hanya, jama'a suna iya duba kayayyakin da ake nunawa, da sayen kayan da suke bukata, yayin da suke zaune a gida. An ce wannan sabuwar hanyar sayar da kaya tana samun ci gaba sosai a kasuwannin kasar Sin, bisa yadda ake kokarin kirkiro sabbin fasahohin sayar da kaya ta shafukan yanar gizo, da yadda jama'ar kasar suka fara sabawa da sayen kayayyaki ta shafin yanar gizo, musamman ma a lokacin da suka yi zaman gida a lokacin da ake samun barkewar cutar COVID-19 a kasar a baya.

Bisa yadda ake samun ci gaba a wannan fanni, ana iya ganin jajircewar tattalin arzikin kasar Sin, da yadda yake samun ci gaba mai inganci. Hakika bangaren sayen kayayyaki ya riga ya zama wani bangare mafi girma da ke taimakawa tabbatar da ci gaban tattalin arzikin kasar. Ana sa ran ganin wannan bangare zai samu karin ci gaba a nan gaba, tare da karuwar bukatun dake akwai game da kayayyaki masu inganci na kasashe daban daban. (Bello Wang)