Rayuwar Stephon Marbury a Beijing da aikin sa karkashin CBA
2020-11-06 08:57:50 CRI
Tsohon dan wasan kwallon kwando, kuma kocin kwallon a yanzu Stephon Marbury, ya kasance daya daga taurarin kwallon kwando da suka shafe tsawon lokaci suna zaune a nan kasar Sin.
Yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a baya bayan nan ya bayyana cewa "Bana jin zai yi ritaya daga horas da kwallon kwando da wuri. Ina ga yanzu ma na fara. Don haka ba batun shirin ritaya a yanzu."
Kocin mai shekaru 43 da haihuwa, wanda ke horas da kungiyar kwallon kwando ta birnin Beijing wato Beijing Ducks, ya shiga shekara ta 10 yana zaune a nan kasar Sin, kuma yanzu yana shirin shafe shekaru goma na gaba a cikin kasar. Stephon Marbury ya ce "bana jin ina cikin mutanen dake son yin ritaya na zauna bana komai tun da wuri. Ina ga idan har ina raye, zan yi aiki har zuwa shekaru 80 zuwa 90. Bana sha'awar zama haka kawai alhali ina raye".
A shekarar 2010 ne dai Marbury ya fara buga kwallon kwando a lardin Shanxi, bayan da har karo biyu, ya kai matsayin manyan 'yan wasan kwallon kwando da ake baje kolin su, yayin bikin hukumar kwallon kwando ta kasa da kasa ta NBA dake Amurka.
Duk da cewa ya fuskanci sauyin al'adu daga tsohuwar kungiyar da ya yiwa wasa wato "New England, zuwa kungiyar sa ta farko a arewacin kasar Sin, sannu a hankali Marbury ya kai ga sabawa da rayuwa a kasar Sin.
A yanzu, shekaru 10 ke nan Marbury na zaune a birnin Beijing, ya kuma shiga kundin tarihin harkar kwallon kwando, wadda hukumar kwallon kwandon kasar wato CBA ke shiryawa. Tun zuwan sa kasar Sin, Marbury ya rungumi kalubalen dake tattare da aiki karkashin CBA, da ma yanayin wasa a kungiyoyin kasar, lamarin da ya kai ga ya samu nasarar fitowa a jerin 'yan wasa mafiya hazaka na hukumar ta CBA har karo 6, tare da kungiyar sa ta Beijing Ducks.
Da yake karin haske game da hakan, Marbury ya ce "Wato a gaskiya na saba da yadda al'umma ke rayuwa a nan, ina yin abubuwa da kowa ke yi. Ina ganin mutane za su fahimci cewa, ba wani abu ne mai wuya ba, ba takura kai a ciki". "Bisa radin kai na na zo nan. Ina son sajewa da kowa. Ina son zama bangaren al'adar wurin,".
Marbury ya kara da cewar, "Idan na waiwayi baya cikin shekaru 10 da suka gabata, sai na ga cewa, zuwa na nan kasar Sin ya zamo mai albarka, domin ban taba zaton zan zo nan na yi wasan kwallon kwando ba. Ban zata zan kai shekaru 10 a nan ba. Ban taba tunanin lashe kofin kwallon kwando a nan ba, balle har a sassaka mutummutumi na, a kuma bani katin zama cikin kasar".
"Mutummutumin nawa, wanda aka sassaka domin martaba gudummawa ta ga kungiyar Beijing Ducks, ya faranta min rai matuka. Kaza lika ya sanya mahaifiya ta matukar farin ciki, lokacin da ta ziyarce ni a birnin Beijing".
Ya ce "Lokaci ne na farin ciki. Lokaci ne na murna ba wai kawai ga mahaifiya ta ba, har ma ga iyalai na gaba daya, saboda abu ne da bai taba faruwa gare mu ba a baya. Mun gode kwarai bisa martaba mu da wannan birni ya yi, lallai samun irin wannan karramawa a wata kasa da ba tawa ba abun alfahari ne. Mun gode hakan, mun bayyana murnar mu kwarai da gaske".
Kari kan wannan Mutummutumi, an kuma baiwa koci Marbury dan asalin kasar Amurka, wata dama da kasafai ake baiwa 'yan kasashen waje ba, wato a shekara ta 2017 an ba shi katin zaman kasa, wanda zai ba shi damar shiga da fita daga kasar ba tare da neman VISA ba.
Ya ce "Da farko ban san mene ne ba. Na ce toh, wannan abu ne mai kyau sosai.' Wato ke nan bana bukatar VISA a duk lokacin da zan fita ko zan shigo kasar Sin. Yayi kyau!. Don haka na yi farin ciki sosai..Ko shakka babu hakan yana da ban sha'awa, ba bukatar sake zuwa neman VISA. Lallai na gode, na kuma jinjinawa kasar Sin. Matsayi ne da duk bako dan kasar waje dake zaune a nan kasar Sin zai yi fatan samu."
A matsayin sa na wanda ya jima a birnin Beijing, Marbury ya koyi al'adun birnin. Tun daga cin abinci a tukunyar tsome, da yawan sayayya a shaguna, duk da ya yi korafi game da cunkoson ababen hawa, da kuma yanayi da a wasu lokaci ke gurbata.
Ya ce "Akwai abu daya da bana so a nan, wanda shi ne cunkoson ababen hawa. Na zo ne daga birnin New York, don haka na saba da yanayin cunkoson ababen hawa, amma na nan daban ne. Batun gurbatar yanayi kuwa, ina ga abu ne da kowa ba ya kauna.
"Ina kallon birnin Beijing kamar yana da yanayi na New York da Washington DC a hade. Mahaifiya ta 'yar Sioux na jihar Maryland ce, wurin da bai wuce tafiyar mintuna 15 zuwa 20 a mota zuwa birnin Washington DC ba. Ina yawan zuwa birnin Washington DC tun ina karami. Ni dan New York ne. Don haka Beijing kamar hadin gambizar wadannan birane biyu ne."
A cikin shekaru 10 da Marbury ya kasance karkashin CBA, Sin ta samu manyan sauye sauye, ta fuskar tattalin arziki da kuma wasan kwallon kwando. A wannan lokaci ne harkar kwallon kwando ta samu babban sauyi da ci gaba, har ta kai an samu matasan 'yan wasa da suka kai matsayin kwarewa a fannin. A lokacin ne taurarin 'yan wasa irin su Zhou Qi, da Sun Minghui, da Abdusalam Abdurexit, da Zhao Jiwei suka haska, wadanda suka kafa wani ginshiki na daga darajar wasan kwallon kwando a kasar Sin.
Koci Marbury ya ce "Tsarin dabarun gudanar da wasan na sauyawa. Yanzu sun fara gane yadda za su gudanar da wasa sabanin da. Tabbas salon wasan su yana sauyawa. Yanzu suna kara karfi, suna kara kwarewa wajen motsa jiki. Matasan yanzu suna sauya salon su gwargwadon sauyawar lokaci. Sabbin masu jini a jiki na tasowa, cike suke da karsashi. Sanin kowa ne cewa suna cike da kuzari, suna da karfin tunkarar wasa, suna kuma kara gane yadda ake buga wasa."
Marbury, wanda ya yi musayar rigar sa ta buga wasa da kayan horas da 'yan kwallon kwando a kasar Sin, ya jagoranci kungiyar "Beijing Royal Fighters" zuwa matsayi na 2 a kakar farko da ya jagoranci kungiyar. Ya kuma sauya matsayin kungiyar daga mai rauni, zuwa kungiyar da ta dare saman rabin teburin kungiyoyi mafiya hazaka na kasar Sin, duk kuwa da yanayin cutar COVID-19 da aka fuskanta a baya bayan nan.
Marbury ya ganewa idanun sa yadda cutar ta haifar da rudani a farko farkon bullar ta. Ya ce "Na yi matukar sa'a, domin kuwa lokacin da aka fara ta a kasar Sin, na tafi Amurka. Kuma lokacin da nake can, mutane ba su gama fahimtar yanayin cutar ba. Na rika fadawa mutane cewa, wannan yanayi ne da ka iya yin tsanani. Bayan nan na bar Amurka na dawo Sin a lokacin da cutar ke daf da fara bazuwa a can, a gabar da kuma Sin ke daf da shawo kan ta. "