logo

HAUSA

Wane sako bikin baje kolin CIIE yake aikewa duniya?

2020-11-06 20:24:04 CRI

Wane sako bikin baje kolin CIIE yake aikewa duniya?

Birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin yana jawo hankalin duk duniya baki daya, inda aka bude bikin baje kolin hajojin da ake shigowa da su kasar Sin ko CIIE a takaice karo na uku. Ganin yadda duniya ke ci gaba da fuskantar barazanar annobar COVID-19, da tawayar tattalin arziki wadda ba safai akan ga irinta ba, kasar Sin ba ta dakatar da bude kofarta ga duniya ba. Abin tambaya a nan shi ne: Wane irin sako bikin CIIE yake aikewa duniya a wannan shekarar da muke fama da matsaloli da dama? Annobar COVID-19 tana kawo babban tsaiko ga ci gaba harkokin duniya, abun da ya sa kasashe da dama a soke manyan tarukan kasa da kasa da suka shirya a baya. Amma kasar Sin ta kaddamar da bikin CIIE na bana kamar yadda aka tsara, al'amarin da ya shaida irin yakinin da muke da shi, na ganin bayan yaduwar annobar da ingantar tsarin shawo kanta.

Wane sako bikin baje kolin CIIE yake aikewa duniya?

A matsayinta na kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, tattalin arzikin kasar Sin ya samu farfadowa kwarai da gaske a watanni 9 na bana, kuma yawan cinikin wajen da ta yi ya karu da kaso 0.7, kana, yawan jarin wajen da take amfani da shi ya karu da kaso 5.2, al'amarin dake zama abun misali ga duniya. Kamar yadda shugaban kungiyar tattalin arzikin kasar Zambiya ya ce, annobar COVID-19 ta sa tattalin arzikin duniya ya fuskanci koma-baya sosai, amma kuma yadda kasar Sin ta kaddamar da irin wannan kasaitaccen biki a daidai wannan lokaci, yana da matukar ma'ana ga farfado da imanin kasa da kasa wajen raya tattalin arzikinsu.

Me ya sa kasar Sin ba za ta rufe kofarta ga kasashen duniya ba, maimakon haka ma, za ta ci gaba da fadada bude kofa ga kasashe daban-daban. Tun da aka yi bikin karo na farko a shekaru 2 da suka wuce, zuwa yanzu, ana ta kara samun 'yan kasuwa gami da kamfanonin kasashe daban-daban wadanda suke son halartar bikin. Shugaban shahararren kamfanin samar da abubuwan kwalliya na kasar Faransa wato L'Oreal, Mista Jean-Paul Agon ya bayyana cewa, a daidai wannan lokaci, duniya na bukatar zama tsintsiya madaurinki daya fiye da duk wani lokaci a da, kuma babu wani abun da zai iya hana kamfaninsa ci gaba da kasuwanci a kasuwar kasar Sin.

Wane sako bikin baje kolin CIIE yake aikewa duniya?

A watan Oktobar bana, an yi cikakken zama na biyar na kwamitin tsakiya karo na 19 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, inda aka tsara shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 14, gami da ajandar neman ci gaba zuwa shekara ta 2035. Kasar Sin ta tsara wani babban shiri, wato idan ana mayar da hankali kan raya tattalin ariki a cikin gida, za a iya hade kasuwar cikin gida da ta ketare domin samun ci gaba mai karfi da dorewa. Irin wannan manufa ta shaida cewa, kasar Sin za ta ci gaba da bude kofa ga kasashen waje, da samar da zaman jin dadi ga al'ummun kasashe daban-daban.

Babu tantama, abin da kasar Sin take yi, na habaka tattalin arziki mai salon bude kofa ga ketare, zai iya kirkiro damammaki da dama, da taimakawa sosai ga ci gaban tattalin arzikin duniya mai dorewa.(Murtala Zhang)