logo

HAUSA

Xi Jinping ya sanar da sabbin matakan kara bude kofar kasar Sin ga duk duniya

2020-11-05 13:05:30 CRI

A jiya, 4 ga wata da dare, an kaddamar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo dasu kasar Sin, wato CIIE karo na 3 a Shanghai. A yayin taron kaddamar da bikin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo.

Xi Jinping ya sanar da sabbin matakan kara bude kofar kasar Sin ga duk duniya

A yayin bikin na CIIE na bana, fadin filayen nune-nunen kayayyaki ya karu da kusan murabba'in mita dubu 30 sakamakon karuwar yawan kamfanonin ketare da yawa. A filin da aka kebe domin nune-nunen kayayyakin kiwon lafiyar jama'a kawai, dimbin manyan kamfanoni wadanda suka fito daga manyan kamfanoni mafi girma guda 500 a duk duniya sun yi baje kolin kayayyakinsu. A cikin jawabinsa, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, a lokacin da kasar Sin take tabbatar da matakan rigakafin bullar annoba, ta shirya wannan kasaitaccen biki wanda yake jawo hankulan duk duniya gaba daya a kan lokaci bisa shiri, ya alamta yadda kasar Sin take kokarin samar da damammakin kasuwanci ga sauran sassan duniya, domin ingiza farfadowar tattalin arzikin duniya baki daya cikin sahihanci.

Xi Jinping yana mai cewa, "Ko da yake annobar COVID-19 ta kawo illa, amma a bana, kasar Sin tana kara saurin bude kofarta ga duk duniya kamar yadda ake fata. Mun aiwatar da dukkan matakan kara bude kofa wanda na shelanta a yayin bikin baje koli karo na biyu da aka shirya a bara. Kasarmu ta kuma ci gaba da shigowa da karin kayayyaki daga ketare. Ana kuma aiwatar da babban shirin gina tashar cinikayya cikin 'yanci a lardin Hainan, da shirin kara yin kwaskwarima da bude kofa a birnin Shenzhen da dai makamatansu bisa shirin kamar yadda ya kamata."

Xi Jinping ya sanar da sabbin matakan kara bude kofar kasar Sin ga duk duniya

Xi Jinping ya nuna cewa, an samu al'amura na rashin tabbas masu dimbin yawa wadanda suke illata tattalin arzikin duniya sakamakon barkewar cutar numfashi ta COVID-19. Ilmin tarihi ya gaya mana cewa, ko da yake akan samu hadarurruka da bala'u daga indallahi, ko wasu tunanin dake nuna adawa da tarihin ci gaban dan Adam, a kullum dan Adam na samun ci gaba. Ya kamata dukkan sassan duniya su yi hadin gwiwa, su tinkari hadarurruka da kalubaloli tare, su kara yin hadin gwiwa da mu'amala, tare da kara bude kofofinsu ga sauran sassan duniya tare.

Xi Jinping ya nanata cewa, "Ya kamata a yi kokarin bude kofa cikin hadin gwiwa domin moriyar juna. Ya kamata a amince da juna maimakon nuna shakku ga juna, ya kamata a hada hannu maimakon fada da juna, ya kamata a kara yin tattaunawa maimakon zargin juna. Sannan, ya kamata a yi kokarin bude kofa cikin hadin gwiwa domin sauke nauyin dake bisa wuyan juna. Ya kamata kasashe masu girma su kasance tamkar abin misali, sauran sassa masu arziki su bi ka'idoji kamar yadda ya kamata, kasashe masu tasowa su kara yin kokarin neman ci gaba. Bugu da kari, ya kamata a yi kokarin bude kofa cikin hadin gwiwa domin daidaita batutuwan duniya tare. Bai kamata mu yarda da matakan kashin kai da na ba da kariya su lallata ka'idoji da odar kasa da kasa ba. Ya kamata a gyara fuskar ka'idojin daidaita batutuwan duniya, ta yadda za a iya bunkasa tattalin arzikin duniya bisa ka'idar bude kofofin sassan duniya ga juna." Xi Jinping ya nuna cewa, a yayin cikakken zama na biyar na kwamitin kolin JKS na 19 da aka rufe shi a kwanan baya, an fitar da shawarar tsara sabon shirin bunkasa kasar Sin na tsawon shekaru biyar masu zuwa na 14. Sakamakon haka, karin bukatun da ake dasu a kasuwannin cikin gidan kasar Sin zasu samar da karin damammaki a kai a kai. Xi Jinping ya nuna cewa, "Kasar Sin babu tantama zata kara bude kofarta daga dukkan fannoni ga duk duniya, sakamakon haka, kasar Sin zata iya kasancewa tamkar wata babbar kasuwar duniya, inda kowa da kowa zai iya cin gajiya tare, gamayyar kasa da kasa zasu iya samun kyakkyawan kuzarin neman ci gaba." Daga karshe dai, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya shelanta cewa, kasar Sin za ta dauki jerin matakan kara bude kofarta ga sauran sassan duniya baki daya.

Xi Jinping ya sanar da sabbin matakan kara bude kofar kasar Sin ga duk duniya

Xi Jinping ya nuna cewa, "Kasar Sin tana son tattaunawa da sauran kasashen duniya wajen daddale ingantattun yarjejeniyoyin cinikayya cikin 'yanci, ingiza hanzarta kulla yarjejeniyar kafa huldar dangantakar tattalin arziki daga dukkan fannoni tsakanin shiyya-shiyya. Sannan a hanzarta tattaunawa tsakanin kasar Sin da kungiyar EU, da kuma tsakanin kasashen Sin da Japan da Koriya ta kudu game da yadda za a iya yin cinikayya tsakaninsu cikin 'yanci. Bugu da kari, kasar Sin zata kara yin mu'amala da koyi da juna da wasu ingantattun yankunan cinikayya marasa shinge. A waje daya, kasar Sin zata yi kokarin halartar aikin yin kwaskwarimar kungiyar cinikayya ta kasa da kasa. A lokaci guda, kasar Sin zata halarci ayyukan hadin gwiwa da MDD, da G20 da kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki ta APEC da kungiyar BRICS za su yi. Daga karshe dai, kasar Sin zata hada kai da wasu kasashen da abin ya shafa wajen samar da ingantattun kayayyakin more rayuwa bisa shawarar 'Ziri daya da hanya daya', domin bunkasa wata al'umma mai makoma daya ga dukkanin bil Adama." (Sanusi Chen)