logo

HAUSA

JKS ta gabatar da shawarar tsara sabon shirin raya kasar Sin na shekaru biyar-biyar (2021-2026)

2020-11-04 09:38:50 CRI

Daga ranar 26 zuwa 29 ga watan Oktoban shekarar 2020 da muke ciki ne, aka gudanar da cikakken zama na 5 na kwamitin tsakiya na 19 na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS), a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda manyan kusoshin jam'iyyar dake rike da ragamar mulkin kasar suka tantance, gami da zartas da shawara game da shirin raya kasa na shekaru 5 masu zuwa, da babban burin raya kasar da ake fatan aiwatarwa nan da shekarar 2035, inda a karshen zaman aka fitar da sanarwar bayan taro.

JKS ta gabatar da shawarar tsara sabon shirin raya kasar Sin na shekaru biyar-biyar (2021-2026)

Sanarwar ta bayyana cewa, shirin raya kasa na shekaru biyar karo na 13 da aka aiwatar daga shekarar 2016 zuwa ta 2020, ya haifar da bunkasar tattalin arziki da fasahohin kasar kana karfin kasar ya kai wani sabon matsayi, baya ga yadda tsarin tattalin arzikin kasar ke ci gaba da inganta.

Shawara da aka zartas a wannan karo, ta nuna wani sabon salo na zamani, da sabbin bukatun da ke akwai, gami da sabbin burin da jama'ar kasar Sin suka sanya a gaba, wadda za ta ba da jagoranci ga aikin raya tattalin arziki da jin dadin al'ummar kasar Sin cikin shekaru 5 da kuma wasu dimbin shekaru masu zuwa. An kuma tabbatar da wani babban burin da aka sanya a gaba, na gina kasa ta zamani dake bin tsarin siyasa na gurguzu, daga dukkan fannoni, inda za a mai da hankali kan neman samun ci gaba mai inganci, da zurfafa gyare-gyare a bangaren samar da kayayyaki, da aikin kimiyya da fasaha, da kirkiro sabbin fasahohi, da habaka bukatu a kasuwannin cikin gida, da tabbatar da samun ci gaba da tsaron kasa.

JKS ta gabatar da shawarar tsara sabon shirin raya kasar Sin na shekaru biyar-biyar (2021-2026)

Wannan shi ne karon farko da aka sanya burin samun cikakken ci gaba a kokarin tabbatar da wadatar da daukacin al'ummar Sinawa. Kana an tsara wasu manyan ayyukan da za a mayar da hankali a kansu, yayin da ake dora muhimmanci kan kasuwannin cikin gida, gami da kokarin tabbatar da cudanyar kasuwannin cikin gida da na kasashen waje.

Haka kuma a yayin wannan zama, an amince da shawarwarin da kwamitin koli na JKS ya gabatar game da shirin raya tattalin arziki da jin dadin jama'a na shekaru biyar-biyar karo na 14, shirin da za a aiwatar daga shekarar 2021 zuwa ta 2025, da manufofin da ake fatan cimma na dogon lokaci zuwa shekarar 2035. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)