logo

HAUSA

Wang Qishan ya taya sabon mataimakin shugaban kasar Seychelles murnar kama aiki

2020-11-04 16:01:27 CRI

Mataimakin shugaban kasar Sin Wang Qishan ya bugawa takwaransa na kasar Seychelles waya don taya shi murnar kama aiki.

Yayin wayar, Wang ya nuna cewa, Sin da Seychelles na da dankon zumunci, kuma suna samun ci gaba mai armash a bangarori daban-daban, ban da wannan kuma suna hadin kai wajen yakar cutar COVID-19 yadda ya kamata. Yana mai fatan hadin kansa da takwaransa don ingiza dangantakar kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi. (Amina Xu)