logo

HAUSA

Babbar kasuwar Sin tana kara jawo hankalin 'yan kasuwar kasa da kasa

2020-11-04 19:29:22 CRI

Babbar kasuwar Sin tana kara jawo hankalin 'yan kasuwar kasa da kasa

Roy, manajan nazari da raya kamfanin samar da kayayyakin madara na Theland dake kasar New Zealand ya bayyana cewa, "Duk da cewa, ana fuskantar matsaloli, amma tabbas za mu je birnin Shanghai domin halartar bikin CIIE, wato bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na uku". Hakika tsokacin da ya yi ya nuna ra'ayin 'yan kasuwar ketare wadanda suka zo nan kasar Sin don halartar bikin CIIE, yayin da suke fama da tasirin da annobar cutar COVID-19 ke haifarwa.

Babbar kasuwar Sin tana kara jawo hankalin 'yan kasuwar kasa da kasa

A yammacin yau, an kaddamar da bikin CIIE karo na uku bisa shirin da aka tsara, wannan babban aikin tattalin arziki da kasuwanci shi ne na daban da aka shirya a kasar Sin, tun bayan bikin hada-hadar ba da hidimomin kasa da kasa na kasar Sin da aka shirya a watan Satumban da ya gabata. Baya ga kasancewar bikin ya nuna wa al'ummun kasa da kasa sakamakon da kasar Sin ta samu wajen dakile annobar COVID-19 ba, yana kuma ingiza farfadowar tattalin arzikin duniya. A cikin shekaru uku da suka gabata, wannan dandalin na hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa mai matsayin koli, ya samu ci gaba a bayyane. Alal misali, fadin cibiyar nune-nune ya kara karuwa da mubara'in mita kusan dubu 30, kuma fadin wuraren nune-nune na manyan kamfanoni 500 mafiya girma a duniya shi ma ya karu da kaso 14 bisa dari, a cikinsu, kamfanoni sama da goma sun halarci bikin ne a karo na farko. An lura cewa, wuraren nune-nunen kayayyakin kiwon lafiya, da magungunan sha sun fi jawo hankalin jama'a, musamman wuraren da aka kebe domin nuna kayayyakin dakile annobar cuta mai yaduwa. A sa'i daya kuma, a karo na farko za a sayar da kayayyakin ta kafar bidiyo kai tsaye, inda za a gayyaci shahararrun taurarin yanar gizo domin su yi talla, ta yadda masu sayayya za su sayi kayayyakin kasa da kasa masu inganci ta kafar bidiyo kamar yadda suke so. Hakika bikin CIIE na kasar Sin yana rika jawo hankalin 'yan kasuwar kasa da kasa a cikin shekaru uku da suka gabata. Manyan kamfanoni 500 mafiya girma a duniya wadanda suka rika halartar bikin sun kai kaso 70 bisa dari, dalilin da ya haka shi ne, sun samu riba mai tsoka a bikin, har ma suna sa ran za su shiga babbar kasuwar kasar Sin a wannan shekara, wadda ke cikin yanayi na musamman.

Ban da haka, dalilin da ya sa bikin ke kara jawo hankalin 'yan kasuwar kasa da kasa shi ne, kokarin da kasar Sin take yi wajen bude kofarta ga ketare. Tun farkon bana, gwamnatin kasar Sin ta fitar da sabbin manufofi a jere, domin kyautata muhallin kasuwanci. Yanzu haka babbar kasuwar kasar Sin wadda ke da yawan al'ummun biliyan 1.4, tana taryen manyan baki daga kasa da kasa ta dandalin bikin CIIE, inda ake sa ran zai ingiza farfadowar tattalin arzikin duniya. (Jamila)