logo

HAUSA

Manufar Sanya Jama'A A Gaban Kome Karfi Ne Mai Tushe Ga Bunkasuwar Kasar Sin

2020-11-03 10:54:56 CRI

Manufar Sanya Jama'A A Gaban Kome Karfi Ne Mai Tushe Ga Bunkasuwar Kasar Sin

An lura cewa, cikin sanarwar da cikakken zama na 5 na kwamitin koli na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin JKS karo na 19 ya gabatar na mai da hankali kan kyautata zaman rayuwar jama'a da kara kudin shigar jama'a da walwalarsu da ba su tsaro da dai sauransu, kalmar jama'a ta bullo har sau 23. Matakin da ya bayyana ra'ayin JKS da gwamnatin kasar Sin na sanya jama'a a gaban kome kuma ya ba da sabon shaida ga al'ummar duniya kan tambayar da ake game da dalilin da ya sa yawan goyon bayan gwamnati a kasar Sin ya kai masayin farko a duniya cikin shekaru 3 a jere.

Tun daga shawarar tsara shirin raya tattalin arziki da kyautata zaman rayuwar jama'a na tsawon shekaru 5 na 14, wato kai wa wani sabon matakin kyautata zaman rayuwar jama'a, zuwa ga burin kai wa matsayin kasa mai matsaikaicin wadata a duniya ta fuskar GDP har ma zuwa muradun habaka mutanen dake da matsakaicin kudin shiga nan da shekarar 2035, duk wadannan matakai na nufin biyan bukatun jama'a. Shawarwarin da aka gabatar a kan taron ya gabatar da ayyuka da dama don cimma wadannan muradu, ciki hadda kara samar da guraben ayyukan yi masu inganci da kara kudin shigar jama'a da raya tattalin arzikin kasar, da kuma kyautata tsarin rarraba kudin shiga da dai sauransu. Abin lura shi ne, karon farko an shigar da burin cimma hakikannin nasarar kyautata zaman rayuwar jama'a cikin muradun taron, ba shakka matakin zai kara inganta walwalar jama'a. Duba da dukkan matakan da Sin take dauka ko za ta dauka nan gaba, kasashen duniya na da imani kuma suna sa rai kan muradun samun bunkasuwa da Sin ta tsara. Dalilin da ya sa Sin ta iya samun irin wannan ci gaba na gani shi ne, gwamnatin ta mai da hankali kan ko wani abu dake da alaka da moriyar jama'a don amfana musu.

Matakin mai da jama'a a gaban kome da tabbatar da zaman rayuwarsu cikin nishadi karfi ne mai tushe dake ciyar da kasar Sin gaba, kuma ita ce shaidar da za ta sa kasashen waje su fahimci matakan da gwamnatin kasar Sin ke dauka. (Amina Xu)