logo

HAUSA

Bikin CIIE zai samar da damammakin raya tattalin arzikin duniya

2020-11-03 13:43:21 CRI

 

Bikin CIIE zai samar da damammakin raya tattalin arzikin duniya

Daga ranar 5 zuwa 10 ga watan da muke ciki, za a gudanar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su cikin kasar Sin (CIIE) karo na 3, a birnin Shanghai dake gabashin kasar. Bikin da ake sa ran zai samar da damammakin raya tattalin arziki na duniya.

Bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su cikin kasuwannin kasar Sin na CIIE wani kasaitaccen biki ne da kasar Sin ta kan gudanar a kowace shekara, wanda ke janyo hankalin 'yan kasuwan kasashe daban daban, wadanda ke neman sayar da kayayyakinsu a kasar Sin. Yanzu haka, cutar COVID-19 ta haifar da wani yanayi na rashin tabbas ga aikin raya tattalin arziki a duniya. Sai dai a nata bangare, kasar Sin ta yi nasarar dakile yaduwar annobar, da ma raya tattalin arzikinta, har ma ta taimaka wajen tabbatar da farfadowar tattalin arzikin duniya, gami da baiwa kanana da matsakaitan kamfanoni na kasashe daban daban damar raya harkokinsu. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taba bayyana cewa, kasar Sin ta yi nasarar raya tattalin arzikinta sosai cikin shekaru fiye da 40 da suka wuce, ta hanyar bude kofarta ga kasashen waje. Saboda haka, a nan gaba kasar za ta kara bude kofarta, don neman samun ci gaban tattalin arziki mai inganci. A matsayin wata shaida ga manufarta ta bude kofa, kasar Sin ta kaddamar da bikin bajekolin kayayyakin da ake shigowa da su cikin kasuwanninta(CIIE) a karo na farko a shekarar 2018. Kana a wannan shekara, duk da cewa annobar COVID-19 na haifar da illa ga tattalin arzikin duniya, amma bikin bajekoli na CIIE na ci gaba da janyo hankalin manyan kamfanoni na kasashe daban daban, wadanda suke son halartar bikin, har wasu daga cikinsu sun kulla kwangila tare da gwamnatin kasar Sin don halartar dukkan bukukuwa na CIIE guda 3 cikin shekaru 3 masu zuwa. Ding Chun, shi ne darektan cibiyar nazarin kasashen Turai ta jami'ar Fudan ta kasar Sin, ya ce, ta hanyar gudanar da bikin bajekoli na CIIE, kasar Sin tana son nunawa al'ummar duniya niyyarta ta bude kofa da yin hadin gwiwa tare da sauran kasashe. Ta yin la'akari da yadda dimbin kamfanoni ke neman halartar biki na wannan karo, a cewar Ding Chun, za a samu damar ciyar da huldar hadin gwiwa dake tsakanin kasar Sin da sauran kasashe gaba, don tabbatar da ci gabansu na bai daya a nan gaba. A wajen bikin CIIE na wannan karo, manyan kamfanoni na kasashe daban daban za su nuna wasu sabbin kayayyaki, da fasahohi na zamani. Kuma wannan shi ne karo na farko da aka nuna su a kasar Sin, da ma daukacin duniya baki daya. Saboda haka masu halartar bikin za su samu damar bude idanunsu, da kara fahimtar sabbin fasahohi masu inganci, wadanda suka shafi aikin kare muhalli, da ciniki mai nasaba da fasahar kwamfuta da shafin yanar gizo na Internet, da fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam, da dai sauransu. Kana za su samu damar ganin yanayin da ake ciki a nan kasar Sin, a kokarin raya kasa ta wasu sabbin tsare-tsare, da neman samun ci gaba mai inganci. Wasu manyan kamfanoni irinsu Michelin, da Schineider Electric SA, da SAP, za su fi mai da hankali kan kokarin nuna wasu sabbin kayayyaki da fasahohinsu, masu alaka da na'ura mai kwakwalwa, da aiki na kare muhalli, a wajen bikinbaje kolin na CIIE. Kana suna neman raya harkokinsu a kasuwannin kasar Sin, cikin wani dogon lokaci mai zuwa.

Hakika biki na CIIE zai zama wata kafa, da mahalarta bikin za su iya ganin wani yanayi mai inganci matuka a fannin raya tattalin arzikin kasar Sin, bisa matakan da ta dauka, na gina yankuna da tashoshi na ciniki cikin 'yanci, da kyautata yanayin zuba jari, da shawarar "Ziri Daya da Hanya Daya", da dai sauransu. (Bello Wang)