logo

HAUSA

Kokarin da Sin take wajen kiyaye muhalli zai taimaka kan gina duniya mai tsabta

2020-11-01 20:28:03 CRI

Kokarin da Sin take wajen kiyaye muhalli zai taimaka kan gina duniya mai tsabta

A cikin shekaru biyar masu zuwa, kasar Sin za ta ci gaba da rage gurbatacciyar iskar da take fitarwa, ya zuwa shekarar 2035, hayaki mai tattare da sinadarin carbon da kasar Sin za ta fitar zai ragu, muhallin halittu masu rai da marasa rai zai kyautata a bayyane, da haka za a cimma burin gina kasar Sin kyakkyawa, a cikin rahoton cikakken taro na biyar na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 19, an bayyana muradun ci gaban kasar cewa, akwai muhimmanci a kara maida hankali kan kiyaye muhallin halittu masu rai da marasa rai da kuma raya kasa ba tare da gurbata muhalli ba, a bayyane an lura anniyar gwamnatin kasar Sin ta nacewa kan manufar raya kasa tare da kiyaye muhalli.

Kasar Sin, babbar kasa ce mai yawan al'ummun biliyan 1.4, hakika gwamnatin kasar Sin tana maida hankali matuka kan aikin kiyaye muhalli a cikin shekaru biyar da suka gabata, alkaluman da hukumomin gwamnatin kasar suka samar sun nuna cewa, yayin da ake kokarin raya kasa tsakanin shekarar 2016 zuwa 2000, adadin hayaki mai tattare da sinadarin carbon da kasar Sin ta fitar ya ragu a kai a kai, kuma makamashi da ba na kwal da man fetur da iskar gas ba ya kai kaso 15.3 bisa dari dake cikin daukacin makamashin da ake amfani da su a nan kasar Sin. A halin yanzu, shugabannin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin suna nacewa kan manufar raya kasa ba tare da gurbata muhalli ba, hukumomin gwamnatin kasar da abin ya shafa sun yi hasasahen cewa, ya zuwa shekarar 2025, adadin GDP da za a samu ba tare da gurbata muhalli ba zai kai kudin Sin yuan triliyan 12, kusan zai kai kaso 8 bisa dari dake cikin daukacin GDP na kasar, ya zuwa shekarar 2035 kuwa, adadin zai kai sama da kaso 10 bisa dari. A matsayinta na babbar kasa a duniya, har kullum kasar Sin tana sauke nauyin kyautata muhalli dake bisa wuyanta, a cikin shekaru biyar da suka gabata, kasar Sin ta fitar da "shirin tabbatar da dauwamammen ci gaba nan da shekarar 2030 na kasar Sin" kafin sauran kasashen duniya, kuma ta yi kokarin ingiza "yarjejeniyar Paris", kana ta cimma burin rage hayaki mai tattare da sinadarin carbon na shekarar 2020 kafin lokacin da ta yi alkawari, ban da haka, a kwanan baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar Sin za ta yi kokari domin cimma burin zuke dukkan iska mai dumama yanayin da kasar ke fitarwa ta hanyar dasa itatuwa da ciyayi nan da shekarar 2060. Mai nazarin manufar makamashi na Amurka Mark Levine yana ganin cewa, burin kasar Sin na zuke dukkan iska mai dumama yanayi ta hanyar dasa itatuwa da ciyayi zai sa kaimi kan sauran kasashen duniya domin su kara daukar matakan da suka dace a bangaren.

Nan gaba kasar Sin za ta ci gaba da samar da dabarunta da karfinta wajen samun dauwamammen ci gaban bil Adama ta hanyar kiyaye muhallin halittu masu rai da marasa rai.(Jamila)