logo

HAUSA

Matakin Da JKS Ya Dauka Na Ba Da Tabbaci Ga Raya Al'umma Da Kyautata Zaman Rayuwar Jama'ar Kasar Sin

2020-10-31 16:21:46 CRI

Matakin Da JKS Ya Dauka Na Ba Da Tabbaci Ga Raya Al'umma Da Kyautata Zaman Rayuwar Jama'ar Kasar Sin

 

Kowa ya sani, Sin ta lashi takobin raya al'ummarta mai matsaikacin wadata da kyautata rayuwar al'umma ba tare da barin kowa a baya ba. To yaya za ta cimma wannan babban buri? Jiya Juma'a, Sin ta gabatar da taron manema labarai a nan birnin Beiijng don bayyana ruhin cikakken zama karo na 5 na kwamitin koli na JKS na 19. Inda mamban kwamitin yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga kasashen waje Ning Jizhe ya nuna cewa, shirin raya tattalin arziki da kyautata rayuwar al'umma na shekaru biyar karo na 14 da Sin za ta gabatar, zai mai da hankali kan kara kudin shiga na wadanda suke karancin samun kudin shiga. To mene ne ma'anar wannan shiri? Wannan shiri na nufin ingiza samun wadata baki daya cikin al'ummar Sinawa, wato gwamnatin kasar Sin za ta yi iyakacin kokarin kara kudin shiga na wadanda suke da karancin samu, da ma habaka yawan mutanen dake da matsakaicin kudin shiga. Matakin da ya kara kyautata zaman rayuwar Sinawa da raya tattalin arzikin kasar Sin, har ma zai yi amfani ga kara kuzarin bunkasuwar tattalin arzikin duniya baki daya. Wannan mataki ba ma kawai zai kara samar da guraben aikin yi, har ma zai inganta guraben aikin yi ga jama'a. Ban da wannan kuma, kara kudin shigar jama'a zai yi amfani wajen samar da damar samun ilmi, ta wannan hanya za a samu wadata daga zuriya zuwa zuriya. Hazalika, samun karin kudin shiga ya baiwa jama'a damar shiga wasannin motsa jiki da samun isashen inshorar jiyya. Dadin dadawa, an ce, za a ba da tabbaci ga samarwa mazauna birane da na kauyuka inshorar rayuwa. Ana iya ganin cewa, ko da yake ana fama da illar cutar COVID-19, amma Sinawa na cin gajiyar matakin da JKS da gwamnatinta suka dauka, duba da cewa ana kara samun kudin shiga da habaka bukatu cikin gida har kasuwanni a kasar na samun farfadowa sannu a hankali. A cikin rubu'i uku na bana, yawan kudin shiga na jama'a ya samu karuwar kashi 0.6%. A watan Satumba kuma, yawan kudin da aka kashe wajen sayen abubuwa ya karu da kashi 3.3% bisa na makamancin lokaci na bara.

An yi imanin cewa, al'umma da kuma tattalin arzikin kasar Sin zai samu farfadowa karkashin jagorancin JKS da gwamnatinta. (Amina Xu)