logo

HAUSA

Har yanzu 'yan siyasan Amurka ba su yi nadamar hasarar da kasar ta tafka a yaki da COVID-19 ba

2020-10-29 21:49:22 CRI

Har yanzu 'yan siyasan Amurka ba su yi nadamar hasarar da kasar ta tafka a yaki da COVID-19 ba

 

"Totally Under Control", wannan shi ne taken shirin bincike game da yaki da annobar COVID-19, wanda sanannen daraktan fim na kasar Amurka Alex Gibney da wasu suka jagoranta, kuma aka nuna shi kwanan nan. A zahiri, taken fim din kansa abin dariya ne na nuna halin ko'in kula ga ayyukan yaki da annobar da shugabannin Amurka ya nuna. Fim din ya lissafa rudani da kura-kurai da gwamnatin Amurka ta tafka a yayin da take tinkarar annobar COVID-19, da kuma yadda ta soki matakin gwamnati na dakile annobar. Ana iya cewa, wannan ya zama muhimmin abin da ke nuna abubuwan dake faruwa a zahiri a fim da talabijin. Ya zuwa yanzu, adadin mutanrn da aka tabbatar sun kamu da annobar COVID-19 a Amurka ya zarce miliyan 8.8, kuma yawan mutanen da suka mutu ya zarce 220,000. A makon da ya gabata kawai, Amurka ta sami sabbin masu kamuwa da cutar sama da 80,000 a cikin kwana guda a cikin kwanaki biyu a jere.  

Har yanzu 'yan siyasan Amurka ba su yi nadamar hasarar da kasar ta tafka a yaki da COVID-19 ba

 

Me ya sa matakan yaki da cutar na kasar Amurka ya durkushe haka? Yayin hira da masana kiwon lafiya, jami'an gwamnati, da masu sa kai, fim din ya bayyana dalilan da suka haifar da masifar daga bangarori daban-daban. Matakan rashin daidaito da masu mulkin Amurka suka dauka su ne abubuwan da suka haddasa tsanantar yaduwar annobar.

Ban da wannan kuma, wani sabon littafi mai suna " American Crisis" da gwamnan jihar New York Andrew Cuomo ya wallafa a kwanan nan, ya yi bayani game da yadda ake samun yaduwar cutar a jihar. A cikin littafin nasa, ya soki gwamnatin Amurka game da "dora laifi" kan kasar Sin da kungiyar WHO, a lokaci guda kuma, ya yi jinjina sosai kan nasarorin da kasar Sin ta samu wajen yaki da annobar, kana ya gode wa kasar bisa ga gudummawar dimbin kayayyakin gaggawa na yaki da annoba da ta baiwa Amurka

Ko shirin bincike daga sanannen darakta ko kuma sabon littafi na gwamnan New York, kusan dukkanin bayanan da aka gabatar sun nuna gaskiyar zalunci: burin siyasa ya fi komai, wannan sune manufar da gwamnatin Amurka ta yi amfani da su yayin da take yaki da annobar. (Bilkisu Xin)