logo

HAUSA

Majalisar Dinkin Duniya ita ce dandalin kara yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa

2020-10-28 09:09:36 CRI

An kebe ranar 24 ga watan Oktoban kowa ce shekara, a matsayin ranar tunawa da kafuwar majalisar, wadda aka kafa bayan yakin duniya na biyu da nufin hana faruwar yake-yake a nan gaba. A ranar 25 ga watan Afrilun shekarar 1945, gwamnatoci kimanin hamsin (50) sun gana a San Fransisco na kasar Amurka, don tattauna yadda za a tsara daftarin dokokin da za su kai ga kafa majalisar, wadda aka amince da shi a ranar 25 ga watan Yunin shekarar 1945, kana ya fara aiki a ranar 24 ga watan Oktoban shekarar 1945, lokacin da MDD ta fara aiki.

Manufar kafa MDD ita ce tabbatar da zaman lafiya a duniya, biyo bayan yakin cacar baka da ya kaure tsakanin Amurka da tsohuwar tarayyar Soviet da kawayensu.

MDD tana da manyan rassa guda shida (6) da suka hada da babban zauren majalisar, da kwamitin sulhu, da hukumar kula da harkokin tattalin arziki, da jin dadin jama'a da kotun kasa da kasa, da sakatariyar majalisar da sauransu.

Haka kuma majalisar na da hukumomi kamar bankin duniya da hukumar lafiya ta duniya (WHO) da shirin samar da abinci na duniya WFP, da UNESCO da UNICEF da makamantansu, an kafa sune da nufin inganta rayuwar al'ummar duniya. Bugu da kari, MDD tana da mambobin kasashe guda biyar dake da kujerun din-din-din da sauran kasashe da ba na din-din-din ba da ake zaba daga lokaci zuwa lokaci na tsawon wani karamin wa'adi, ta yadda za a kara janyo kasashen mambobin majalisar a jika, don sanin bukatunsu da yadda za a warware dukkan matsaloli da suke fuskanta. A bana ne majalisar ke cika shekaru 75 da kafuwa, kuma daga wancan lokaci zuwa yanzu, majalisar ta ba da gagarumar gudummawa ga ci gaban rayuwar bil-Adama a fannoni daban-daban. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)