logo

HAUSA

A yi hattara kar a Garin neman Kiba a Nemo Rama

2020-10-28 18:48:11 CRI

A yi hattara kar a Garin neman Kiba a Nemo Rama

 

A yayin da wasu kasashe ciki har da kasar Sin suka yi nasarar dakile bazuwar annobar COVID-19, da ma kokarin da suke yi na samar da allurar rigakafin annobar, a hannu guda wasu kasashen yamma har yanzu na fama da wannan annoba. Sai dai kuma a kwanakin baya babban darektan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya yi kira da a yi hattara, game da salon da ake son amfani da shi na yiwa mafi yawa na al'ummar duniya allurar rigakafin cutar COVID-19, duba da irin matsaloli da kalubale da salon ke tattare da shi a tsari na kimiyya. Wai kar a garin neman Gira a rasa Ido. A kimiyance, ana amfani ne da salon yiwa al'umma mafiya rinjaye rigakafi domin ba su kariya daga wata cuta da aka riga aka fahimta. Misali ana bukatar yiwa kaso 95 bisa dari na al'ummar duniya allurar rigakafin kyanda, domin samar da kariya daga harbuwa daga cutar, wadda a irin wannan yanayi ake fatan ragowar kaso 5 da suka rage, ba za su kamu da ita ba. Kaza lika irin wannan salo yana ba da kariya ne ga mutane, ba wai ba su damar fuskantar cutar ba kariya ba. Kuma a tarihi ba a taba amfani da wannan salo wajen magance annobar da ta barke ba. Sanin kowa ne cewa, har yanzu duniya ba ta da cikakkiyar masaniya game da dabarun kare jikin bil Adama daga harbuwa da annoba COVID-19, wadda ya zuwa yanzu ke ci gaba da halaka rayuwa da kawo illa ga harkokin tattalin arziki da sauran fannoni na rayuwar bil-Adama, ta ke kuma neman gagarar kwandila. Abu mafi muhimmanci shi ne, a daina siyasantar da batun annobar COVID-19, don neman biyan bukatu na kashin kai. Maimakon haka, ya dace kasashen duniya su hada kai a dukkan fannoni, don ganin bayan wannan annoba.

Abin farin ciki shi ne, yadda kasashen duniya suka shiga shirin COVAX da hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO, da kawancen shirin samar da allurar rigakafi na duniya ke jagoranta, hakan ya shaida hadin gwiwar kasa da kasa da a kullum bangaren Sin yake fatan ganin dorewarsa, ta yadda za a gudu tare a tsira tare. (Ibrahim Yaya)