logo

HAUSA

Ziyarar malam Aliyu Abubakar a Beijing(B)

2020-10-27 14:33:32 CRI

Ziyarar malam Aliyu Abubakar a Beijing(B)

A makon da ya gabata, Murtala Zhang ya tattauna da Aliyu Abubakar, jami'in hulda da jama'a dake aiki a babban kamfanin man fetur na Najeriya, wato NNPC, inda malam Aliyu Abubakar ya bayyana yadda ziyararsa a kasar Sin ta kasance, wato lokacin da ya zo halartar taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka ko kuma FOCAC a takaice a shekara ta 2018 a birnin Beijing. Malam Aliyu Abubakar ya ce ya ga babban ci gaban da kasar Sin ta samu, kuma ya taba ziyartar wasu wurare masu ban sha'awa a Beijing, ciki har da babbar ganuwa wato Great Wall. Game da taron FOCAC kuma, Aliyu Abubakar ya ce, taro ne mai amfani kwarai da gaske, musamman wajen inganta hadin-gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Haka kuma ya bayyana wasu daga cikin kusoshin gwamnati a tawagar Najeriya da suka halarci taron a wancan karo.

A cikin shirin na wannan sati, malam Aliyu Abubakar ya yi karin haske kan hadin-gwiwar da ake yi tsakanin Sin da Najeriya, da yadda jama'a za su ci gajiya daga irin wannan hadin-gwiwa.(Murtala Zhang)