logo

HAUSA

Renon Furen Nasara--Sana'o'in mata na bada gudunmuwa wajen gina karkara a yankin San Gua

2020-10-26 17:02:55 CRI

Kungiyar mata ta yankin raya tattalin arziki na Chaohu dake birnin Hefei, babban birnin lardin Anhui na gabashin kasra Sin, ta dauki matakai a shekarun baya-bayan nan, wajen bunkasa sana'o'in mata da kirkire-kirkire da kuma taimakawa mata lalubo hanyoyin yaki da talauci. Wadannan matakai sun hada da shirya darussan horo da samar da titi mai lakabin sana'o'in mata da kuma samar da dabarun tallafi ga mata. Bisa la'akari da tallafin kungiyar mata, matan da suka fara kasuwanci a Unguwar al'ummar San Gua, wani sanannen wurin yawon bude ido a yankin raya tattalin arziki na Chaohu sun zama masu "renon furen nasara". An kafa kungiyar mata ta yankin raya tattalin arziki na Chaohu ne a ranar 7 ga watan Maris na 2017. Karkashin Jagorancin kungiyar ta mata, Unguwar al'ummar San Gua ma ta kafa kungiyar mata.

Bisa manufar bayyana ainihin albarkatun yankunan karkara, San Gua ta hada aikin gina yankin da raya ayyukan gona da kasuwanci da al'adu da bude ido. San Gua na da wani sanannen titi, wato titi mai lakabin sana'o'in mata.

Akwai gomman shaguna a kan titin. Kungiyar mata ta San Gua ta samar da dabarun tallafi dake karfafawa mata fara kasuwanci. Misali, ba sa bukatar biyan kudin haya da na ruwa da na lantarki a farkon bude shago. Galibin matan da suka fara kasuwanci a kan titin, mata ne da aka bari a garuruwansu domin su kula da iyalansu. Akwai kuma matan da suka kammala kwaleji da wadanda suka fito daga wasu yankuna. Ga matan da suka riga suka koyi fasahohi da kuma samar da kayayyakin da suke sayarwa da kansu, kungiyar mata ta San Gua na samar da dabarun da za su taimaka musu bunkasa kasuwancinsu. Ga wadanda ba su riga sun koyi fasahohi ba kuma, kungiyar kan taimaka wajen bude musu shaguna da samar musu da kayayyakin da za su sayar, da aka samar a San Gua kan farashi mai rahusa. A baya-bayan nan, mata na taka muhimmiyar rawa wajen ginawa da raya garuruwansu. Shekaru 4 da suka gabata, Zhou Weiqin na rayuwa kamar yadda galibin mata dake garin ke yi. Ta ce, "na kan bi mijina ci rani. Ba ni da lokacin kula da yara da tsoffin dake iyalinmu. Matasan kauyenmu na tafiya birni don kyautata rayuwarsu. Tsoffi ne ke zama a kauye. Suna noman kayayyakin lambu da shinkafa, don su ciyar da kansu".

A shekarar 2016, ta samu labarin cewa, yankin San Gua na horar da 'yan kasuwa, wadanda ake karfafa musu gwiwar bude shaguna a wannan wuri na kasuwanci da yawon shakatawa. Zhou ta kware wajen dafa Mahua (wani nau'in abincin Sinawa). A wannan lokaci, tana ganin komawa garinsu ta bude shagon sayar da Mahua shawara ce mai kyau. Sai dai, ba ta san yadda za ta gyara tare da kawata gida ya koma shago ba. kuma ba ta san yadda za ta kula da shago ba. Ta yi sa'a, kungiyar mata ta San Gua ta taimaka mata.

Mambobin kungiyar mata sun ba Zhou shawarar yadda za ta samar da kayayyaki, kuma sun taimaka mata gina shago da karfafa mata gwiwar halartar darussan horo, domin koyon dabarun gudanar da sana'o'i a karkara ta intanet. A halin yanzu, Zhou ta mallaki shagon sayar da Mahua. Yawan kudin da shagon ke samu a shekara ya zarce yuan miliyan 5, kwatankwacin dala dubu 700.

Shen Lei ma na gudanar da kasuwanci a San Gua. An haifi Shen ne a Chaohu a shekarar 1992. Ita da iyayenta sun koma Suzhou, na lardin Jiangsu dake gabashin kasar Sin ne a lokacin da take da shekaru 2 a duniya. Shen ta yi kewar garinsu na Chaohu, a lokain da take tasowa.

Shen ta ce, "a shekarar 2015 aka kafa San Gua. Na ziyarci wannan harabar a shekarar 2016. Na dauki lokaci ina shawarar komawa mahaifata. Fara kasuwanci abu ne da ya bambanta sosai da aiki a karkashin wani. Kana bukatar tunani da yawa idan kai ne shugaba." Shen ta fara kasuwanci ne a shekarar 2017, a lokacin tana da shekaru 25. Dabarun taimako na kungiyar ya ba Shen kwarin gwiwar zama a San Gua. Bayan shekara daya tana aiki tukuru, Shen ta samu ma'aikata, wadanda suke sayar da kayayyaki tare ta kafar intanet. "muna sayar da amfanin gona da kayayyakin makulashe da aka sarrafa a San Gua. Daga nan ake samar da kayayyakin. Ma'aikatana na taimakawa mutanen kauyenmu sayar da amfaninsu na gona". Zuwa yanzu, an bude shaguna 19 a kan titin kasuwanci na mata a San Gua. Masu shagunan sun hada sarrafa amfanin gona da raya cinikayya ta kafar intanet da yawon bude ido.

Wacce rawa mata ke takawa wajen bunkasa yankunan karkara da yaki da talauci? Ta yaya za a ja hankali tare da karfafawa mata, musammam matasa, gudanar da kasuwanci a garuruwansu? Domin amsa wadannan tambayoyi, kungiyar mata ta yankin raya tattalin arziki na Chaohu ta shirya wasu shirye-shirye daban-daban, dake sa mata kaunar yankunan karkara da taimaka musu lalubo dabarun raya kasuwancinsu.

Kungiyar matan na gudanar da darussa da bayar da horo ga matan kauyuka, ta yadda za su samu bayanai dangane da harkokinsu na gona da cinikayya ta intanet da yawon bude ido. Baya ga haka, matan karkara kan shiga shirye-shirye masu armashi kamar da tarukan karatu da wasannin kwaikwayo da shirya furanni da koyon sabbin dabaru da fadada tunaninsu da fahimta.