logo

HAUSA

Mai Adalci Shi Zai Samu Nasara

2020-10-23 20:28:57 CRI

 

Mai Adalci Shi Zai Samu Nasara

 

Idan wata rana, bata gari suka shiga gidan makwabcinka, suna masa musgunawa da zalunci, yaya za ka yi? Shin kana da jan hali da zai sa ka fito ka taimaki makwabcinka, don kare adalci? Wasu shekaru 70 da suka wuce, Sinawa sun taba yin haka, inda suka yi babbar sadaukarwa, tare da samun nasara a karshe.

Bayan babban yakin duniya na biyu, kasar Koriya dake makwabtaka da kasar Sin ta rabu zuwa kasar Koriya ta Arewa, mai bin tsarin siyasa na gurguzu, da Koriya ta Kudu, dake bin tsarin jari hujja. Sa'an nan a shekarar 1950, an samu barkewar rikici tsakanin Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu. Ganin haka ya sa kasar Amurka ta so yin shisshigi a yakin, don tabbatar da matsayinta na mai cikakken tasiri da jagoranci a nahiyar Asiya. Saboda haka, kasar Amurka ta yi kokarin sanyawa a kafa wata runduna ta MDD, inda yawancin sojojin rundunar na kasar Amurka ne, don taimakawa Koriya ta Kudu wajen yakin. A sa'i daya kuma, kasar Amurka ta tura manyan jiragen ruwa na yaki, don su shiga mashigin tekun Taiwan, don hana sojojin kasar Sin 'yantar da tsibirin Taiwan. Ban da wannan kuma, kasar Amurka ta yi kokarin mallakar wurare daban daban na Koriya ta Arewa, har ma ta kai wutar yaki zuwa kan iyakar Koriya ta Arewa da kasar Sin. Ganin yadda sojojojin kasar Amurka ke kai hari ga makwabciyarta, gami da takalar ta da fada, kasar Sin ta nuna sanin ya kamata da adalci. A watan Satumban shekarar 1950, mista Zhou En'lai, firaministan kasar Sin a lokacin, ya gabatar da wani jawabi, inda ya yi gargadi ga kasar Amurka, cewa: " Jama'ar kasar Sin sam ba za su yi hakuri kan harin da wata kasa za ta kai musu ba, kana idan wata babbar kasa ta nemi kai hari ga makwabtanta, to, kasar Sin ba za ta yarda a yi hakan ba." Sai dai a nasa bangare, babban kwamandan sojojin kasar Amurka Douglas MacArthur, yana ganin cewa, kasar Sin za ta ji tsoron fito-na-fito da kasar Amurka. Saboda haka, ko da yake gwamnatin kasar Sin ta yi gargadi har sau da dama, amma MacArthur, ya yi biris da gargadin, tare da ci gaba da kai hare-hare a zirin Koriya. Hakika a shekarar 1950, akwai babban gibi tsakanin kasar Sin da kasar Amurka, a fannin karfin tattalin arziki. A lokacin matsakaicin kudin shiga na Sinawa shi ne kimanin dalar Amurka 24 a duk shekara, amma wannan adadi a kasar Amurka ya kai fiye da dalar Amurka 1600. A shekarar 1950, kasar Sin tana iya samar da karfe ton dubu 600 ne a shekara, yayin da kasar Amukra ta kan samar da karfe kimanin ton miliyan 88 a kowace shekara. Ta wandannan alkaluma, za mu iya ganin cewa, bisa yanayin da take ciki a lokacin, kusan ba zai yiwu ba kasar Sin ta samu nasara a wani yaki da kasar Amurka. A lokacin shugabannin kasar Sin su ma sun yi tattaunawa kan ko za a tura sojojin don taimakawa Koriya ta Arewa, inda aka samu sabanin ra'ayi sosai. Sai dai a karshe, niyyar da kasar Sin ta dauka, ta kare adalci, da tsaron gida, ta sa ta yanke shawarar tura sojoji zuwa zirin Koriya, don turjewa zaluncin Amurka. A watan Oktoban shekarar 1950, kasar Sin ta kafa rudunar sojoji masu sa kai, tare da tura su zuwa zirin Koriya don halartar yaki. Bayan wasu kazaman fadace-fadace da aka kwashe shekaru 2 da watanni 9 ana yinsu, sojojin kasar Sin sun samu nasarar korar abokan gaba, daga bakin kogin Yalu, dake kan iyakar Sin da Koriya ta Arewa, zuwa tsohon layin kan iyaka da aka shata a tsakanin Koriya ta Arewa, da Koriya ta Kudu, suka tilastawa abokan gabansu sa hannu kan wata yarjejeniyar tsakaita bude wuta, ta yadda aka samu dawo da zaman lafiya a zirin Koriya. Duk wannan yaki ne da ya haifar da asarar rayuka. Bisa kididdagar da aka yi, wasu sojojin kasar Sin fiye da 197,000 sun sadaukar da rayukansu a fagen yaki na zirin Koriya. Wadannan sojoji sun sadaukar da kansu don tabbatar da adalci a duniya, da tsaron kasarsu. A nasu bangare, sojojin Amurka da farko dai sun yi zaton cewa, Sinawa za su ji tsoron yaki da su, daga baya kasar Sin ta tura sojoji, sa'an nan Amurkawa sun fara tsammanin cewa, ba zai yiwu ba sojojin Sin su yi nasara a kan su. Sai dai a karshe dai, bisa kokarin yaki da Sojojin Sin da Koriya ta Arewa suka yi da su, sojojin Amurka ba su da abin yi, sai su yi watsi da yunkurin su na kai hari kan Koriya ta Arewa, da karbar shawarar tsagaita bude wuta. Kafin ya sa hannu kan wannan yarjejeniya ta daina yaki, janar na kasar Amurka Mark Wayne Clark, ya ce, shi kadai ne janar din kasar Amurka da ya sa hannu, kan wata yarjejeniyar tsagaita bude wuta, a wani yaki da kasar Amurka ba ta yi nasara a cikin sa ba. A yau Juma'a, an yi bikin cika shekaru 70, tun bayan da sojojin Sin suka taimaka wa Koriya ta Arewa, wajen turjewa zaluncin Amurka, a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce, ba za a manta da shahidan da suka rasa rayukansu a yakin ba, kana yadda kasar Sin ta halarta gami da cin nasara a wannan yaki, ya nuna niyyar Sinawa na adawa da mulkin danniya, da matsayarsu ta kiyaye zaman lafiya a duniya.

Ko da a baya, ko a yanzu, ko kuma a nan gaba, za a rika samun damar ganin mai adalci ya ci nasara a karshe. (Bello Wang)