An tono asirin ASPI
2020-10-22 16:35:22 cri
A kwanan baya, jam'iyyar Australian Citizens Party ta wallafa wani bayani a shafinta na yanar gizo, inda ta tono asirin cibiyar nazarin tsare-tsare ta kasar Australia na yaudarar jama'a don cimma burin siyasa. Bayanin ya kara da cewa, yanzu cibiyar ta karkata hankalinta ga kasar Sin, kuma jerin matakan da ta dauka tamkar yadda aka yada jita-jitar wai "akwai miyagun makaman kare dangi a kasar Iraki".
Cibiyar nazarin tsare-tsare ta kasar Australia(ASPI) ta jima da fakewa da sunan masanan nazari wajen biyo bayan 'yan rukunin masu nuna kyamar kasar Sin wadanda ke kokarin samar da rahotannin rashin gaskiya don shafa wa kasar Sin bakin fenti. Bayanin da jam'iyyar Australian Citizens Party ta wallafa a shafinta na yanar gizo, ta bayyana cewa, cibiyar nazarin tsare-tsare ta Australia (ASPI) ta samu jarinta ne daga majalisar gudanarwar kasar Amurka da ma gwamnatocin wasu kasashen waje da kungiyar NATO, har ma da wasu kamfanonin samar da makamai na kasa da kasa, kuma burin cibiyar shi ne ta tilasta wa gwamnatin kasar don ta bi 'yan rukunin masu nuna kyamar kasar Sin wajen shafawa kasar Sin bakin fenti. A cewar jam'iyyar, cibiyar na taka muhimmiyar rawa wajen lalata huldar dake tsakanin kasashen Sin da Australia.
Hasali ma dai, a karshen watan Satumba, jam'iyyar Australian Citizens Party ta wallafa jerin rahotanni a shafinta, inda ta tono yadda cibiyar ASPI da ma kungiyoyin 'yan leken asiri na kasar suka yi ta hura wutar nuna kyamar kasar Sin a cikin 'yan shekarun baya a yunkurin lalata huldar da ke tsakanin Sin da Australia.A cewar bayanin, kungiyoyin 'yan leken asiri na kasar Australia sun yi ta yayata kalaman na wai "barazanar da ake fuskanta daga kasar Sin", tare da yiwa kasar Sin suka bisa wasu abubuwan da ba a tabbatar da su ba, don boye halin da ake ciki game da yadda kungiyoyin 'yan leken asirin kasar Australia da ma kungiyar five eyes alliance suka samu iko a manufofin diplomasiyya na kasar Australia, da ma yadda suka yada bayanan rashin gaskiya ga al'ummar kasar.
Baya ga haka, kafar yada labarai mai zaman kanta ta APAC ta kasar Australia ma ta ba da karin haske cewa, cibiyar ASPI ta samu miliyoyin daloli daga gwamnatoci da kuma kamfanoni na kasashen waje, ciki har da wani babban kaso da ta karba daga kamfanonin da suka tilastawa fursunonin gidan yari aiki don cin riba. Abin dariya kuma shi ne, cibiyar tana zargin kasar Sin da laifin take hakkin bil Adam.
Ta kuma kara da cewa, cibiyar ASPI tana kara fuskantar suka daga tsoffin jami'an diplomasiyya da na tsaro da manyan masharhanta na kasar. (Lubabatu)