logo

HAUSA

KUSKURE NE "KURA TA CE DA KARE MAYE"

2020-10-22 17:24:52 CRI

 

KUSKURE NE "KURA TA CE DA KARE MAYE"

Masu fashin baki da dama na ci gaba da ganin baiken yadda Amurka ke kururuta cewa, wasu kasashen duniya na mata leken asiri, duk kuwa da cewa, shaidu da dama sun nuna cewa ita ce ma kan gaba wajen aikata wannan laifi.

Wasu rahotanni sun nuna cewa, hukumar tsaron kasar ta CIA na amfani da wani kamfanin kasar Switzerland mai suna Crypto AG, wajen tattara bayanan sirri na al'ummun dake sassan duniya da dama. To sai dai duk da wannan zargi da ake wa Amurka, a hannu guda mahukuntan ta sun fito fili a baya bayan nan, suna zargin kasar Sin da yiwa Amurkan leken asiri. Wannan zargi ya baiwa mahukuntan kasar Sin matukar mamaki, inda har aka jiyo kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian, na kira ga Amurka, da ta daina zargin kasar Sin da laifin da ita ce ke aikata shi. Jami'in ya ce a baya bayan nan, hukumar tsaron Amurka ta (NSA), ta zargi Sin da kasancewa barazana ga bayanan tsaron ta. Ya kara da cewa, ko sau nawa aka maimaita karya, ba za ta sauya matsaya ta koma gaskiya ba. Don haka lokaci ya yi da Amurka za ta dakatar da zargi kan laifin da ita ce ke aikatawa. Idan dai ba a manta ba, mai kwarmata bayanan nan na WikiLeaks wato Edward Snowden, ya taba bayyana cewa, Amurka ta shafe tsawon lokaci tana tattara bayanan biliyoyin mutane ta wayoyin salula da suke amfani da su, har ma Snowden din ya ce akwai lokacin da Amurka ta nadi bayanan sirri daga wayar salula da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ke amfani da ita. Idan mun yi duba kan wadannan zarge-zarge da ake yiwa mahukuntan Amurka, za mu fahimci cewa, kamata ya yi su fara wanke kansu, ta hanyar yin cikakken bayani game da kalaman na Mr. Snowden, kafin su samu bakin zargin wasu kasashe na daban da yi wa Amurka leken asiri. A nata bangare kuwa, Sin ta sha nanata cewa, ba ta da tunani ko aniyar yiwa wata kasa leken asiri, kasancewar hakan ya sabawa dokokin cudanyar kasa da kasa, kuma bai dace ko wace kasa ta aikata hakan ba. Kaza lika mahukuntan Sin, sun sha nanata bukatar gabatar da shaidu na zahiri, wadanda za su tabbatar da zargin na Amurka, idan kuwa ba bu shaidu, to lokaci ya yi da Amurkan za ta dakatar da wannan kalamai na bata suna, da yunkurin shafawa kasar ta Sin kashin kaji.

Ko shakka babu, dogaro da wadannan shaidu da rahotanni, kan matakai daban daban da kasar Amurka ke dauka domin bata sunan kasar Sin, muna iya cewa ko alama, bai dace ma "Kura ta ce da kare maye" ba. (Saminu Hassan)