logo

HAUSA

Dandalin FOCAC alamar hadin gwiwa ce dake tsakanin kasashe masu tasowa

2020-10-21 14:42:38 CRI

A wannan shekarar ce, dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka wato FOCAC ya cika shekaru 20 da kafuwa, dandalin dake zama babbar alamar hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa.

Daga shekarar 2000 da wanzuwar wannan dandali zuwa yanzu, bangarorin biyu sun tsaya tsayin daka wajen raya al'ummominsu, da dukufa wajen inganta dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare a tsakaninsu. Haka kuma, sakamakon da aka cimma a tarukan FOCAC sun taimaka matuka ga al'ummomin Sin da Afirka.

Ga mai bibiyar nasarorin dandalin na FOCAC, zai fahimci cewa, Sin da Afirka sun cimma matsayi daya wajen karfafa hadewar al'ummominsu waje guda, lamarin da ya taimaka ga bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka. A karkashin wannan dandalin, kasar Sin ta fito da jerin matakan taimakawa Afirka a fannonin samar da muhimman kayayyakin more rayuwa, da suka hada da layin dogo, da hanyoyin mota, da filayen jiragen sama, da tashoshin jiragen ruwa, da filayen wasanni na zamani, da musayar kwararru, aikin gona, al'adu da makamantansu.

Sai dai, duk da nasarorin da sassan biyu suka cimma, wasu kasashen yammacin duniya, na yiwa wannan kyakkyawar dangantaka bahaguwar fahimta, a wasu lokuta ma suke neman bata dangantakar da ke kara bunkasa a dukkan fannoni.

A shekara mai zuwa ne, za a shirya taron dandalin FOCAC na gaba a kasar Senegal, taron da masana suka yi imanin cewa, zai taimakawa Sin da Afirka wajen cimma burinsu na bai daya, tare da bayyana muhimmancin cudanyar bangarori daban-daban da kullum kasar Sin ke shelar bukatar dorewarsa a duniya. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)