logo

HAUSA

Hali Zanen Dutse

2020-10-21 19:50:21 CRI

 

Hali Zanen Dutse

 

Mai hali dai aka ce baya sauyawa, duk da bayanai da shaidu da muhimman takardu da tawagogin masana da 'yan jaridu suka gabatar game da ziyarar da suka kai a yankin Xinjiang da sauran sassan kasar Sin, amma har yanzu wasu kasashe yamma ba su gamsu da ma daina neman shafawa kasar Sin kashin kaji ba. Komai aka yi da Jaki, Ai sai ya ci Kara.

A baya wani masanin kasar Sin ya wallafa bayanai game da yanayin aiki yi na kananan kabilu dake zaune a yankin na Xinjiang da yadda ake kare 'yanci da hakkokinsu amma duk da haka, wasu masana daga kasashen yamma sun wallafa wasu rahotanni a kwanakin baya dake cewa, wai ana samun karuwar tilasta aikin kwadago a yankin Xinjiang na kasar Sin, kana wasu 'yan siyasar yammacin duniya ma, na ikirarin cewa, "Ana tilasta aikin kwagado a Xinjiang". Abin tambaya shi ne, akwai zargin tilasta aikin kwadago a Xinjiang? Kan wannan batu, cibiyar bincike dake Xinjiang, ta gayyaci kwararru da masana, domin su bincike yadda kananan kabilu ke gudanar da aikin kwadago a yankin na Xinjiang. Tawagar ta ziyarci sama da kamfanoni 70, da kamfanonin gama kai dake yankunan karkara da wuraren sana'o'i na daidaikun mutane da aka kafa a Ili, da Karamaya, da Shihezi, da Kashgar da Hotan, da Kizilsu da kuma Aksu dake Xinjiang da kuma birane dake wajen shiyyar, kamar Beijing da Tianjin. Sun kuma tattauna tare da hira da sama da manajojin kamfanoni da ma'aikata da masu sana'o'i masu zaman kansu da ma'aikata kananan kabilu sama da 800, sun kuma nazarci muhimman takardun gwamnati 26 da aka gabatar tun a shekarar 2016, da takardun da abin ya shafa 48 da masana suka wallafa tun a shekarar 2005. Daga karshe, tawagar ta bayyana cewa, gwamnatoci a dukkan matakai da kamfanonin da abin ya shafa a Xinjiang da sauran larduna ko birane, sun taimakawa 'yan kananan kabilu samun guraben ayyukan yi, sun kuma kare dukkan hakkokinsu, kamar 'yancin samun aikin yi da na ci gaba.

Rukunin kananan kabilu suna aiki ne bisa radin kansu, sun kuma zabi kafa sana'o'insu na kansu, don haka batun wai, ana tilastawa mutane aikin kwadago, bai ma taso ba. Zargin da wasu masanan kasashen yamma ke yi, karye ce kawai, kuma ikirarin da suke yi kan wannan batu, ba shi da tushe balle makama. Amma abin ka da wanda ya yi nisa, aka ce baya jin Kira.(Ibrahim Yaya)