logo

HAUSA

Shin 'Yan Siyasan Kasashen Yammacin Duniya Za Su Ci Gaba Da Yin Karya Kan Yankin Xinjiang?

2020-10-20 21:20:11 CRI

A 'yan kwanakin baya, kwalejin nazarin manufofi da manyan tsare-tsare na kasar Australiya, wadda ke samun tallafin kudi daga 'yan adawar kasar Sin, ta kaddamar da wani rahoto kan yankin Xinjiang na kasar Sin, inda ta shafa wa kasar Sin kashin kaji da cewa, ana tilasta wa mutane masu yawa su yi aiki a yankin. Sa'an nan wasu 'yan siyasan kasashen yammacin duniya sun bata sunan yankin Xinjiang ta fuskar kiyaye hakkin dan Adam bisa lamarin. Sun kuma sossoki kasar Sin game da manufofinta kan Xinjiang. A daren ranar 19 ga wata, cibiyar nazarin ci gaban yankin Xinjiang ta kasar Sin, ta kaddamar da rahoton bincike kan aikin kananan kabilu a yankin Xinjiang, inda a cewarta, ana mutunta burin 'yan kananan kabilu na samun aikin yi, ana kuma kiyaye hakkokinsu na yin aiki da samun ci gaba. Duk da ganin dimbin abubuwan shaida, shin wadannan masana da 'yan siyasar kasashen yammacin duniya za su ci gaba da yin karya? Alkaluman kididdiga sun nuna cewa, daga shekarar 2013 zuwa karshen shekarar 2019, yawan mutane masu fama da talauci ya ragu zuwa kaso 1.24 ciki 100, daga kaso 19.4 cikin 100 bisa jimilar yawan mutanen yankin na Xinjiang. An kiyasta cewa, ya zuwa karshen wanann shekara, za a fitar da dukkan mazauna yankin Xinjiang daga kangin talauci. Haka kuma 'yan kananan kabilu mazauna yankin sun kara samun kudin shiga ta hanyar ci rani a wasu sassan kasar. Bisa abubuwan da aka tanada, cikin rahoton bincike kan aikin kananan kabilu a yankin Xinjiang, 'yan kananan kabilu mazauna yankin suna aiki cikin mutunci, lamarin da ya zama wata alama ce ta ci gaban sha'anin kare hakkin dan Adam na Xinjiang, kana kuma kyakkyawan sakamako ne da kasar Sin ta samu wajen aiwatar da manufofin yankin. Kasashen duniya sun amince da hakan.

Duk wata karya da bata suna ba za ta sauya aniyar 'yan kananan kabilu mazauna yankin Xinjiang ta yin aiki cikin mutunci, da samun zaman rayuwa mai kyau ba. Yankin Xinjiang mai wadata da kwanciyar hankali, zai musanta duk wata karya da aka yi masa. (Tasallah Yuan)