logo

HAUSA

Kafofin watsa labarai da masana Afirka sun karyata jita-jitar wai Sin na leken asiri a kasashensu

2020-10-20 10:57:59 cri


A watan Mayun bana, asusun Heritage na masu sassaucin ra'ayi na Amurka dake birnin Washington na Amurka, ya wallafa wani rahoto mai taken "Da alamun yan leken asirin kasar Sin na aikin leken asiri a manyan gine-ginen gwamnatocin kasashen Afirka", inda aka bayyana cewa, kasar Sin tana neman samun bayanan siyasa da tattalin arziki ta hanyar samar da tallafi wajen gina ko gyara manyan gine-ginen gwamnatocin kasashen Afirka, amma kafofin watsa labarai da masanan da abin ya shafa na kasashen sun karyata jita-jitar da ba gaira ba dalili da ake bazawa.

Kafofin watsa labarai da masana Afirka sun karyata jita-jitar wai Sin na leken asiri a kasashensu

Rahoton na asusun masu sassaucin ra'ayi na Amurka ya bayyana cewa, kasar Sin tana neman samun bayanan siyasa da tattalin arziki na kasashen Afirka ne ta hanyar samar da tallafi wajen gina ko gyara manyan gine-ginen gwamnatocin kasashen a kalla guda 186, tare da kafa tsarin yanar gizo a cikin gwamnatocin kasashen a kalla 14, ko kuma bayar da na'urorin kwamfuta kyauta ga gwamnatocin kasashen Afirka a kalla 35, kana rahoton ya kara da cewa, gwamnatin kasar Sin ta yi haka ne domin neman samun fifikon takara ga kamfanoninta a nahiyar Afirka, tare kuma da cimma yunkurinta na sa ido kan jami'an kasashen yamma dake wakilci a kasashen Afirka da kuma yin tasiri ga jami'an kasashen Afirka, an sha ruwaito rahoton a kafofin watsa labarai, yanzu haka yayin da ake murnar cika shekaru 20 da kafa dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, an sake baza jita-jitar wai kasar Sin tana leken asiri a kasashen Afirka, duk wadannan sun nuna cewa, an yi haka ne domin lalata huldar sada zumunta dake tsakanin sassan biyu wato Sin da Afirka.

Kafofin watsa labarai da masanan da abin ya shafa na kasashen Afirka su ma sun karyata jita-jitar.

Kafofin watsa labarai da masana Afirka sun karyata jita-jitar wai Sin na leken asiri a kasashensu

Jaridar "Authority" ta tarayyar Najeriya ta wallafa wani rahoto mai taken "Rahoton karya na asusun Amurka yana gabatar da labarai ba gaira ba dalili" a ranar 12 ga wata, inda ake zargi cewa, babu shaidu ko kadan a cikin rahoton, dalilin da ya sa ya fitar da wannan rahoton shi ne domin karuwar tasirin kasar Sin a nahiyar Afirka ta rage kwarjinin Amurka a Afirka, kuma yana ganin cewa, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka yana kawo hadari ga Amurka, har ma ya bukaci kasashen Afirka da su gujewa hadarin da kasar Sin ke kawo musu, makasudin wallafa rahoton shi ne domin kiyaye moriyar siyasa da tattalin arziki ta Amurka a nahiyar Afirka. Hakika rahoton jaridar ta Najeriya ya tono ainihin makasudin asusun na goyon bayan gwamnatin Trump wato tana mai da hankali kan moriyar Amurka a Afirka kawai, a bayyane an lura cewa, ya wallafa rahoton ne domin lalata huldar hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Afirka, a karshe dai, jaridar ta nuna cewa, ya dace masanan da abin ya shafa na kasa da kasa su yi bayani kan ainihin huldar dake tsakanin Sin da Afirka domin kawar da shakku da ake nunawa, kana kamata ya yi sassan biyu wato Sin da Afirka su ci gaba da gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninsu ta hanyar gina kyakkyawar makomar bai daya ta Sin da Afirka, domin amfanin al'ummun sassan biyu baki daya.

Kana a ranar 16 ga wata, masanin kimiyyar siyasa da huldar kasa da kasa na jami'ar Abuja ta Najeriya Ibrahim ya wallafa wani rahoto mai taken "Hasashen da ake yi kan huldar dake tsakanin Sin da Afirka" a wasu manyan kafofin watsa labarai na kasar Ghana, inda ya karyata ra'ayin karyar wai kasar Sin tana satar bayanan gwamnatocin kasashen Afirka, kuma ya jaddada cewa, baza jita-jitar dake nuna kyamar kasar Sin zai kara karfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka ne kawai.

Kafofin watsa labarai da masana Afirka sun karyata jita-jitar wai Sin na leken asiri a kasashensu

Ban da haka, jaridar "Gold Street Business" ta kasar Ghana ta wallafa wani sharhi a ranar 16 ga wata cewa, rahoton da asusun na Amurka ya fitar wai kasar Sin tana satar bayanan Afirka ta hanyar samar da tallafi ga kasashen Afirka wajen gina manyan gine-ginen more rayuwa ba shi da tushe ko kadan, hakika kasashen yamma, sun dade suna sa ido kan gwamnatocin kasashen Afirka, domin kara habaka tasirinsu a nahiyar da kuma fadin duniya baki daya. Kasashen Afirka suna da 'yancin zabar abokan hadin gwiwa, yanzu haka kasashen Afirka sun zabi kasar Sin saboda kasar Sin tana da dogon tarihi kuma tana samun ci gaban tattalin arziki cikin sauri a cikin 'yan shekarun da suka gabata.

Kamar yadda aka sani, kasar Sin tana samar da taimako ga kasashen Afirka ba tare da gindaya wani sharadin siyasa ba, a cikin 'yan shekarun da gabata, kasar Sin ta samar da tallafi ga kasashen Afirka a fannin yaki da cutar Ebola, yanzu haka tana taimakawa kasashen wajen dakile cutar COVID-19, duk wadannan sun nuna cewa, amincin dake tsakanin sassan biyu yana kara zurfafa, zargi maras tushe da asusun Amurka ke bazawa ba zai yi tasiri ga hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu ba, kuma ra'ayin nuna kyamar kasar Sin zai kara karfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka kawai.(Jamila)