Fasahar dinki ta gargajiya ta kabilar Yi ta taimakawa matan kabilar wajen kawar da talauci (A)
2020-10-13 18:59:36 CRI
Kwanan baya, ni da malama Fa'iza Mustapha da kuma Murtala Zhang mun ziyarci gundumar Zhaojue, ta jihar Liangshan mai cin gashin kai ta kabilar Yi dake kudu maso yammacin kasar Sin, inda muka fahimci yadda kungiyar hadin kan mata ta gundumar suke gudanar da ayyukansu musamman ma a fannin kawar da talauci, ciki har da kafa kwasa-kwasai kyauta ga gidan renon yara, da kafa kasuwar musamman a kauyuka don kara wa mazauna wurin gwiwar kafa dabi'a mai kyau, da kuma tattaunawa da mata don fahimtar halin zaman rayuwa da suke ciki da dai sauransu. A yayin ziyarar kuma, shugabar kungiyar hadin kan mata ta gundumar ta kuma baiwa Fa'iza da Murtala ayyukan da jami'an kungiyar suke yi a yau da kullum, don taimaka musu kara fahimtar yadda ayyukansu suke. To, a cikin shirinmu na yau, za su tattauna game da ziyarar nan.