logo

HAUSA

Kasashe da sassan tattalin arziki gaba daya 171 sun shiga shirin COVAX

2020-10-12 13:07:13 cri


A yayin wani taron manema labaru da WHO ta shirya a kwanan baya, Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus, babban direktan WHO ya bayyana cewa, kawo yanzu kasashe da sassan tattalin arziki gaba daya 171 sun shiga "shirin samarwa gami da rarraba allurar rigakafin cutar COVID-19", wato COVAX a takaice, sakamakon haka, bayan an yi nasarar nazari da kuma samun allurar, kasashe da sassan tattalin arziki wadanda suka shiga wannan shiri za su iya samun allurar bisa tsarin shirin.

Kasashe da sassan tattalin arziki gaba daya 171 sun shiga shirin COVAX

Game da wannan ci gaban da aka samu wajen aiwatar da shirin COVAX, Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa, "A farkon lokaci, yawan allurar rigakafin cutar babu yawa, amma za a rarraba su cikin daidaito bisa shirin. Dukkan kasashe da sassan tattalin arziki za su iya rarrabawa mutanen da suka fi matukar bukata, kamar ma'aikatan aikin jinya, da tsofaffi da kuma mutane marasa lafiya wadanda ya kamata su riga sauran mutane samun allurar. Bisa shirin, za a tabbatar da samarwa da kuma rarraba allurar kimanin biliyan 2 ya zuwa karshen shekarar 2021."

Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus ya nuna cewa, a lokacin da ake dakile cutar numfashi ta COVID-19, dole ne a tuna cewa, ana kuma fuskantar barazanar sauran cututtuka daban daban, kamar mutuwar jarirai a lokacin haihuwa, da ake samu a kowace rana, cutar COVID-19 ta tsananta wannan halin da ake ciki. Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus ya kara da cewa, bisa rahoton da asusun yara na MDD, da bankin duniya, da kungiyar WHO suka fitar kwanan baya, yawan jarirai da ake haifa babu rai a kowace shekara ya kai kusan miliyan 2.

"Rahoton ya bayyana cewa, yawan matsalolin haihuwar da babu rai da suka faru a kasashe marasa karfin tattalin arziki ya kai kashi 84 bisa dari sakamakon rashin ingancin tsarin kula da mata masu juna biyu. Za a iya magance faruwar galibin matsalolin, amma barkewar annobar COVID-19 ta tsananta girman matsalolin. Ana samun karuwar mata masu juna biyu dake mutuwa a lokacin haihuwa."

A waje daya, Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus ya nuna cewa, annobar COVID-19 ta kuma kawo illoli sosai ga miliyoyin mutane wadanda suka kamu da cutukan tabin hankali. Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi nuni da cewa, "Yawan mutanen da suka kamu da cutukan da suka shafi tabin hankali ya kai kusan biliyan 1 a duk fadin duniya. Yanzu ana samun mutum guda dake kashe kansa a duk dakika 40. Amma har yanzu a duk fadin duniya, mutane kalilan ne ke iya samun ingantacciyar jinyar tabin hankali. A kasashe marasa karfin tattalin arziki, mutanen da suka kamu da cutukan dake da nasaba da tabin hankali kuma basu samu kulawa ko kadan ba sun kai kashi 75 bisa dari. Ya zama wajibi a canja irin wannan halin da ake ciki. Yanzu lokaci ne da ya kamata a zuba makudan kudade a fannin kulawa da masu fama da cutukan tabin hankali, ta yadda za a iya tabbatar da ganin masu tabin hankalin sun samu ingantaciyyar jinya kamar yadda ya kamata."

Kasashe da sassan tattalin arziki gaba daya 171 sun shiga shirin COVAX

Bugu da kari, a yayin taron manema labaru, madam Maria Van Kerkhove wadda ke kula da harhohin fasaha na shirin gaggawa na hukumar WHO ta bayyana cewa, duk wanda ya kamu da cutar COVID-19 zai iya magance sake samun cutar a cikin wasu lokuta, amma har yanzu ba a iya tabbatar da daidai wa'adin da zai iya magance ta ba. Sannan tabbas ne ba zai yiwu a iya magance sake kamuwa da ita har abada ba.

Game da batun shigar da kasar Sin cikin shirin COVAX, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta ce, kasar Sin ta shiga wannan shiri ne, domin ganin an rarraba allura cikin daidaito da adalci da tabbatar da cewa, za ta samarwa kasashe maso tasowa, tare kuma karfafawa sauran kasashe gwiwar shiga wannan shiri. Hua ta ce, ta wannan hanya Sin za ta kara yin hadin gwiwa da sauran kasashe da yankuna a wannan fanni.

Hua Chunying kuma ta kara da cewa, Sin za ta kara hada kai da kasashe da yankuna da suka shiga wannan shiri, don taka rawar gani wajen yakar cutar da kiyaye rayuka da lafiyar jama'a a kasashe daban-daban na duniya. (Sanusi Chen)